Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da ManzonSa* Ya bã ku rabo biyu daga rahamarSa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama.
____________________
 * Manzon Allah a nan, shi ne Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Anã umarnin ma'abũta Littãfi da su bĩ shi dõmin su sãmi rabo ninki biyu. Mãsu ĩmani a nan su ne 'Ahlul Kitãbi' na ƙwarai.


الصفحة التالية
Icon