Da tsararrun auren* wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya** da shi a bãyan farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
____________________
* An haramta muku matan auren wasu maza, matuƙar mazansu ba su sake su ba, Musulmi ne kõ kuwa Kitãbãwa, sai fa idan kun kãmo su ne daga ƙasar da take ta abõkan gaba, a nan kunã iya tãkinsu haka, dõmin kãmu yã warware aurensu. Idan kun yi tamattu'ida wasu mãtã a kan kuskure, ba da aure ba, sai ku biya su sadãki a kan haka. An hana auren tamattu'i, watau yin aure zuwa ga ajali. Abdullahi bn Abbas ya ce yin sa yã fi zina. ** Bãyan sadãkin da aka yanka bãbu laifi ĩdan kun yi yardatayya da ƙãra wani abu a kan farilla, kuma bãbu laifi idan ita matar tã yarda da kãyar da ƙarin kõ kuwa shĩ mijin ya yarda da biyan ƙãrin.


الصفحة التالية
Icon