surah.translation .

An-Nazi'at


Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.

Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.

Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.

Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.

Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.

Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.

Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.

Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.

Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.

Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?

"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"

Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"

To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.

Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.

Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?

A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?

Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.

"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.

"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?"

Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.

Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),

Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.

Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.

Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."

Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.

Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.

Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.

Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.

Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.

Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.

Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.

Da duwatsu, Yã kafe ta.

Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.

To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.

Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.

Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.

To, amma wanda ya yi girman kai.

Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).

To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.

Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.

To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.

Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?

Me ya haɗã ka da ambatonta?

Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.

Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.

Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.