Ash-Shu'ara' 26:189

سورة الشعراء

Meccan Verse: 189/227 Page 375

فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمِ ٱلظُّلَّةِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٍ ١٨٩

  1. Hausa translation

    الترجمة الهوساوية

    Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije* ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.
     * An ruwaito cewa Allah Ya bũɗe musu ƙõfar Jahannama, zãfi ya hana su zama akõ'ina cikin gidãjensu, sa'an nan aka sanya girgije ya yi musu inuwa mai sanyi-sanyi har suka tãru a ciki, sa'an nan aka sanya girgijen ya kãma da wuta a kansu suka ƙõne kurmus kamar an gasa fãra. Suka kõma tõka kamar yadda suka nema daga Shu'aibu da a jefa musu ɓaɓɓake daga sama idan ya zama daga mãsu gaskiya.

Read the whole surah Compare translations Arabic tafsir