۞ وَمَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُكَلِّمَهُ ٱللَّهُ إِلَّا وَحۡيًا أَوۡ مِن وَرَآيِٕ حِجَابٍ أَوۡ يُرۡسِلَ رَسُولࣰا فَيُوحِيَ بِإِذۡنِهِۦ مَا يَشَآءُۚ إِنَّهُۥ عَلِيٌّ حَكِيمࣱ ٥١
Ash-Shura 42:51
سورة الشورى
Meccan
Verse: 51/53
Page 488
-
Hausa translation
الترجمة الهوساوية
Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana* fãce da wahayi, kõ daga bãYan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima.
* Annabãwa a lõkacin da Allah Ya yi musu magana ba su gan shi ba, sai dai sun ji maganarsa kamar yadda Musã ya ji, kõ kuma da wãsiɗar malã'ika kamar sauran Annabãwa, kõ kuwa da ilhama watau ya san hukunci ba da magana kõ wani wãsiɗar malã'ika ba. Ilhãmar Annabãwa da mafarkinsu gaskiya ne. Ilhãma da mafarkin sauran mutãne bã ya zama hujja sai idan yã dãce da shari'a, sai a yi aiki da shi a kan shari'a bã a kan mafarkin ko ilhãmar ba. -
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana fãce da wahayi, kõ daga bãYan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima.
Ash-Shura 42:51
Loading the recitation…
0:00