فَلَمَّا جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَرِحُواْ بِمَا عِندَهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ ٨٣
Ghafir 40:83
سورة غافر
Meccan
Verse: 83/85
Page 476
-
Hausa translation
الترجمة الهوساوية
A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi* kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi ya wajaba a kansu.
* Ilmin dũniya na sanã'õ'i ya zõ ne daga Annabãwa kamar na ibãdu. Nũhu ya fãra sassaƙar jirgin ruwa da wahayi daga Allah, Zulƙarnaini ya fãra haɗa baƙin ƙarfe da gaci dõmin hana tsãtsa, Yũsufu ya fãra barin hatsi a cikin sõshiya dõmin hana ƙwãri. Dãwũda ya fãra sanã'ar sulke. Ãdam ya fara rubũtu, Idirĩsu ya fara yin alƙalami. ĩsã ya fãra warkar da majinyata, Alƙur' ãni ya nũna anã iya tãshi sama da jirgin sama. Shu'aibu shi ya nũna kasuwanci, da sauransu. -
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi ya wajaba a kansu.
Ghafir 40:83
Loading the recitation…
0:00