ترجمة معاني سورة الطارق باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.*
____________________
  * Wannan ya yi kama da zuwan Annabi a cikin jahiliyya don ya haskaka duniya da ilimi kamar yadda girgije ke ba da ruwa saboda tsiron ƙasa, hantsar uwa ta ba da nono saboda jariri kuma maniyi ya zo lokacin Jima'i.
Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
Rãnar da ake jarrabawar asirai.
Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,*
____________________
  * Dõmin fitar tsiro.
Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki*
____________________
  * Mai rabewa tsakanin ƙarya da gaskiya.
Kuma shĩ bã bananci* bane
____________________
* Kãkãci.
Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.