surah.translation .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

(Wannan) sũra ce. Mun saukar da ita, kuma Mun wajabta ta, kuma Mun saukar da ãyõyi bayyanannu a cikinta, dõmin ku riƙa tunãwa.
Mazinãciya da mazinãci,* to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu.
____________________
  * Hukuncin waɗanda ba su yi aure ba ne, amma waɗanda suka yi aure hukuncinsu a jefe su har su mutu, bãyan sharuɗɗa sun cika, kamar yadda yake ga sunna. Kuma wannan ga hakkin 'ya'ya ne, amma bãyi, hukuncinsu bũlãla hamsin kawai.
Mazinãci bã ya aure* fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai.
____________________
  * Auren mazinãci kõ mazinãciya makarũhi ne ga wanda bahakanan yake ba, dõmin tsaron mutunci da kõre tuhuma.
Kuma waɗanda ke jĩfar* mãtã masu kãmun kai, sa'an nan kuma ba su jẽ da shaidu huɗu ba to, ku yi musu bũlãla, bũlãla tamãnin, kuma kada ku karɓi wata shaida tãsu, har abada. Waɗancan su ne fãsiƙai.
____________________
 * Haddin ƙazafi bũlãla tamãnin ga ɗã, kõ arba'in ga bãwa idan ya yi ƙazafi ga ɗã,.
Fãce waɗanda suka tũbadaga bãyan wannan, kuma suka gyãru, to lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Kuma waɗanda ke jĩfar mãtan* aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su ba, fãce dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah, 'Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga magasganta.'
____________________
 * Hukuncin ranstuwar li'ani da yadda ake yin ta.
Kuma ta biyar cẽwa 'La'anar Allah ta tabbata a kansa, idan ya kasance daga maƙaryata.'
Kuma yanã tunkuɗe mata azãba ta yi shaida, shaida huɗu da Allah, 'Lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga maƙaryata.'
Kuma tã biyar cẽwa 'Hushin Allah ya tabbata a kanta idan ya kasance daga magasganta.'
Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku, da rahamarSa, kuma cẽwa Allah Mai karɓar tũba ne, Mai hikima!
Lalle ne waɗanda* suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã'a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sanã'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma.
____________________
 * Farko Hadĩsil Ifk ne wanda waɗansu suka jefi Ã'isha, Ummul Mũminĩna da zina a cikinsa Allah Ya barrantar da ita. Bai zama sharri ba ga Musulmi, sai dai ya zama alheri dõmin ya zama sanadi ga sanin hukunce-hukunce mãsu yawa, na zaman jama'a da kuma darajar mutãnen da abin ya shãfa. Yadda ƙissar take shi ne yadda Ã'ishatu, Uwar Mũminai ta faɗa, ta ce: "Na kasance tãre da Annabi tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, a cikin wani yãƙi, a bãyan an saukar da Hijãbi, watau kulle. Sai ya ƙãre daga yãƙin ya kõma, ya yi kusa da Madĩna, sai ya yi umurni da tãshi ga tafiya a wani dare, sai ni kuma na tafi na ƙãre sha'anĩna, na fuskanta zuwa ga wurin rãƙumãta, sai na ga abin wuyana ya yanke, saina kõma, na neme shi, kuma su mãsu kula da ni suka ɗauki darbũka suka aza a kan rãkuma sunã zaton inã ciki alhãli mãtã sun kasance sauƙãƙa dõmin ba su cin kõme sai kaɗan na abinci." Na sãmi abin wuyãna na kõmo a bãyan sun tafi. Sai na zaunaa masaukĩna wanda na kasance a ciki. Kuma na yi zaton mutãnen zã su rasa ni su kõmo zuwa gare ni. Sai na ji barci na yi barcin. Shi kuma Safwãnu ya yi rurumi daga bãyan ãyarin yãƙi, ya fita da sauran dare sai ya wãyi gari a inda nake. Sai ya ga duhun mutum mai barci, sai ya gãne ni a lõkacin da ya gan ni, dãmã ya kasance yanã ganĩ na a gabãnin kulle, sai na farka da jin sautinsa na istirjã'i. "A lõkacin da ya gãne ni, sai na rufe fuskãta da mayãfina. Wallãhi bai yi mini magana ba da kalma, ni kuma ban ji kõ kalma ba daga gare shi, sai dai istirjã'insa a lõkacin da ya gurfanar da rãƙumarsa, ya take ƙafarta ta gaba, ni kuma nã hau, ya shiga yanã jan rãƙumar da ni har muka isa ga uwar yãƙin, a bãyan sun sauka, a cikin zãfin rãna. Daga nan wanda ya halaka ya halaka, wanda ya jiɓinci girman abin, shi ne Abdullahi bn Ubayyi bn salũl. "Buhãri da Muslimu sun ruwaito shi.
Don me a lõkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai mãta ba su yi zaton alhẽri game da kansu ba kuma su ce: "Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?"
Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kãwo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata.
Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira. Lalle ne, dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a cikinsa.
A lõkacin da kuke marãbarsa da harsunanku kuma kunã cẽwa da bakunanku abin da bã ku da wani ilmi game da shi, kuma kunã zaton sa mai sauƙi alhãli kuwa, shi a wurin Allah, babba ne.
Kuma don me a lõkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, "Bã ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne mai girma"?
Allah Yanã yi muku wa'azi, kada ku kõma ga irinsa, har abada, idan kun kasance mũminai.
Kuma Allah Yanã bayyana muku ãyõyinSa, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
Lalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhãli kuwa, kũ ba ku sani ba.
Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa. Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne, Mai jin ƙai!
Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni, kada ku bi hanyõyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin hanyõyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yanã umurni da yin alfãsha da abin da ba a sani ba, kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, bãbu wani mutum daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yanã tsarkake wanda Yake so kuma Allah Mai ji ne, Masani.
Kuma kada* ma'abũta falala daga gare ku da mawadãta su rantse ga rashin su bãyar da alhẽri ga ma'abũta zumunta da miskĩnai da muhãjirai, a cikin hanyar Allah. Kuma su yãfe, kuma su kau da kai. shin, bã ku son Allah Ya gãfarta muku, alhãli Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?
____________________
  * Mai yin alheri dõmin Allah kada ya yanke shi daga wanda yake yi wa alherin nan, sabõda yã yi masa wani laifi, da ya shãfe shi ga mutuncinsa kõ dũkiyarsa. Sai ya yãfe, ya kau da kai, ya ci gaba da alherinsa dõmin Allah, kamar yadda Mistahu, wanda yake a cikin dangin Abũbakar As-siddiƙ ya shiga a cikin Hadĩsil Ifk alhãli kuwa Abũbakar ke ciyar da shi sabõda shi misĩkini ne da zumuntã kuma a tsakãninsu, sai Abũbakar ya gãfarta masa, kuma ya ci gaba da bã shi abin da yake bã shi. Haka sauran wuɗanda suka fãda a cikin wannan masifa, an yãfe musu a bãyan an yi musu haddin ƙazafi, sai dai wanda ya ɗauki mai girmansa, wãtau Ibn Ubayyu, shi kam ba a yi masa haddi ba dõmin Allah Ya yi masa alkawarin azãba mai tsanani a Lãhira. Watau Musulmi ake yi wa haddi dõmin ya tsarkaka.
Lalle ne waɗannan da suke jĩfar mãtã mãsu kãmun kai gãfilai* mũminai, an la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma sunãda azãba mai girma.
____________________
   * Gãfila, ita ce wadda ba ta jarrabi kõme ba sabõda ƙurucciya.
A rãnar da harsunansu da hannãyensu, da ƙafãfunsu suke bãyar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
a rãnar dl Allah Yake cika musu sakamakonsu tabbatacce kuma sunã sanin (cẽwa) lalle Allah, Shi ne Gaskiya bayyananna.
Miyãgun mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun* maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan mãtã suke. waɗancan sũ ne waɗanda ake barrantãwa daga abin da (mãsu ƙazafi) suke faɗa kuma sunã da gãfara da arziki na karimci.
____________________
  * Haka miyãgun kalmõmi bã su dãcewa sai daga mũgun mutum. Kuma kalmõmin ƙwaraiba su fitõwa sai daga mutãnen ƙwarai.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai kun sãmi izni, kuma kun yi sallama* a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare ku, tsammaninku, zã ku tuna.
____________________
* Hukuncin shiga gidãje da neman izni da sallama.
To, idan ba ku sãmi kõwa a cikinsu ba, to, kada ku shige su, sai an yi muku izni. Kuma idan an ce muku, "Ku kõma." Sai ku kõma, shi ne mafi tsarkaka a gare ku. Kuma Allah game da abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
Bãbu laifi a kanku, ga ku shiga gidãje waɗanda bã zaunannu ba, a cikinsu akwai waɗansu kãya nãku. Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke nũnãwa, da abin dakuke ɓãyẽwa.
Ka ce wa mũminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjõjinsu.* wannan shĩ ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sanã'antãwa.
____________________
 * Hukuncin tsare idãnu da rũfe al'aura ga maza da mãtã.
Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan* ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo.
____________________
 * Mãtansu, watau mãtã Musulmi banda mãtã kãfirai, bã ya halatta ga mace kãfira ta ga al'aurar mace Musulma. Mabiya sũ ne mãsu nħman bukãta ga mãtã wãtau miskĩnai, tsõfaffi daga maza. Al'aurar mace, ɗiya a cikin salla kõ a tãre da wani namiji ajnabi, to, dukan jikinta ne sai fuska da tãfuna, haka kuma a cikin salla. Amma a tãre da mace Musulma tsakãnin cĩbiya da guiwõyi, shi ne al'aura, kuma tãre da muharraminta, dukan abin da bã sasanni ba. Baiwa kamar namiji take, al'aurarsu abin da ke tsakãnin cĩbĩya da guiwa.
Kuma ku aurar da gwaurãye daga gare ku, da sãlihai daga bãyinku, da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadãtar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani.
Kuma waɗannan da ba su sãmi aure ba su kãme kansu har Allah Ya wadãtar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansã idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu kuma ku bã su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bã ku. Kuma kada ku tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu,* dõmin ku nẽmi rãyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a bãyan tĩlasta su, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
____________________
  * Tsaron kai, shi ne su yi aure; tĩlastãwa a nan, shi ne a hana su aure dõmin su yi wa ubangijinsu aiki.
Kuma lalle ne Mun saukar zuwa gare ku, ãyõyi mãsu bayyanãwa, da misãli daga waɗanda suka shige daga gabãninku, da wa'azi ga mãsu taƙawa.
Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misãlin HaskenSa, kamar tãgã, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi taurãro ne mai tsananin haske, anã kunna shi daga wata itãciya mai albarka, ta zaitũni, bã bagabashiya ba kuma bã bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma kõ wuta ba ta shãfe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misãlai ga mutãne, kuma Allah game da dukan kõme, Masani ne.
A cikin waɗansu gidãje waɗanda Allah Yã yi umurnin a ɗaukaka kuma a ambaci sũnansa a cikinsu, sunã yin tasbĩhi a gare Shi a cikinsu, sãfe da maraice.
Waɗansu maza, waɗanda wani fatauci bã ya shagaltar da su, kuma sayarwa bã ta shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsai da salla da bãyar da zakka, sunã tsõron wani yini wanda zukãta sunã bibbirkita a cikinsa, da gannai.
Dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Ya ƙãra musu daga falalarsa. Kuma Allah Yanã azurta wanda Yake so, bã da lissafi ba.
Kuma waɗanda suka ƙãfirta ayyukansu sunã kamar ƙawalwalniyã ga faƙo, mai ƙishirwa yanã zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kõme ba, kuma ya sãmi* Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisãbinsa. Kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne.
____________________
  * Ya sãmi Allah a wurin da ƙawalwalniyar take, alhãli Allah Ya gaya masa cħwa bãbu ruwa a nan, kuma Ya nũna masa hanyar da zai sãmi ruwa, idan zai bĩ ta. Sai Allah Ya cika masa hisãbinsa da cħwa, "Allah Mai saurin sakamako ne ga wanda ya sãɓa wa umurninSa," Dõmin nan da nan mai sãɓawar zai ga kuren kansa, tun daga dũniya. HisãbinAllah yanã aukuwa da sauri a kan mai sãɓã wa umurninsada gangan.
Kõ kuwa kamar* duffai a cikin tẽku mai zurfi, tãguwar ruwa tanã rufe da shi, daga bisansa akwai wata tãguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai sãshensu a bisa sãshe, idan ya fitar da tãfinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai sanya masa haske ba, to, bã ya da wani haske.
____________________
 * Ayyukan kafiri, wanda bã ya bin Hasken Allah ga aikinsa kamar mai ƙishirwa da wanda ya siffanta a sama yake, kõ kuwa kamar mai tafiya a cikin duffan da aka siffanta a wannan ãya.
Shin, ba ka gani ba (cẽwa) lalle ne Allah, Wanda yake a cikin sammai da ƙasa sunã yi Masa tasbĩhi, kuma tsuntsaye sunã mãsu sanwa, kõwane lalle ya san sallarsa da tasbĩhinsa kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa?
Mulkin sammai da ƙasa ga Allah kawai yake, kuma zuwa ga Allah makõma take.
Ashe, ba ka ganĩ ba, lalle ne Allah Yanã kõra girgije, sa'an nan kuma Ya haɗa a tsakãninsa sa'an nan kuma Ya sanya shi mai hauhawar jũna? Sai ka ga ruwa yanã fita daga tsattsakinsa, kuma Ya saukar daga waɗansu duwãtsu a cikinsa na ƙanƙarã daga sama, sai ya sãmu wanda Yake so da shi, kuma Ya karkatar da shi daga barin wanda Yake so. Hasken walƙiyarsa Yanã kusa ya tafi da gannai.
Allah Yanã jũyar da dare da yini. Lalle ne a cikin wannan akwai abin kula ga ma'abũta gannai.
Kuma Allah ne Ya halitta kõwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan cikinsu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan ƙafãfu biyu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya akan huɗu. Allah Yãna halitta abin da Yake so, lalle Allah, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne.
Lalle ne haƙĩƙa Mun saukar da ãyõyi, mãsu bayyanãwa. Kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya.
Kuma sunã cẽwa, "Mun yi ĩmãni da Allah da kuma Manzo, kuma mun yi ɗã'ã." Sa'an nan kuma wata ƙungiya daga gare su, su jũya daga bãyan wancan. Kuma waɗancan ba mũminai ba ne.
Kuma idan aka kirã su zuwa ga Allah da ManzonSa, dõmin Ya yi hukunci* a tsakãninsu, sai gã wata ƙnngiya daga gare su sunã mãsu bijirewa.
____________________
  * Wannan yanã nũna cewa rashin yardã da hukuncin Allah kãfirci ne. Wanda ya kai ƙãra ga kõtun al'ada alhãli kuwa yanã Musulmi kuma ya halatta haka, bã da wata lalũra ba, ya zama kãfiri sai idan ya tũba. Bã ya halatta ga Musulmi su yarda da yin kõtunanal'ãda a ƙasarsu.
Kuma idan hakki ya kasance a gare su, zã su jẽ zuwa gare shi, snnã mãsu mĩƙa wuya.
Shin, a cikin zukãtansu akwai cũta ne, ko kuwa sunã tsõron Allah Ya yi zãlunci a kansu da ManzonSa? Ã'a, waɗancan sũ ne azzãlumai.
Maganar mũminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa dõmin Ya yi hukunci a tsakãninsu takan kasance kawai su ce "Mun ji, kuma mun yi ɗã'ã, Kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara."
Kuma wanda ya yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsõron Allah, ya kuma bĩ Shi da taƙawa to waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu, 'Lalle ne idan ka umurce su haƙĩƙa sunã fita.' Ka ce, "Kada ku rantse, ɗã'ã sananna ce! Lalle ne, Allah Mai ƙididdigewã ne ga abin da kuke aikatãwã."
Ka ce: "Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu. Kuma bãbu abin da yake a kan Manzo fãce iyarwa bayyananna."
Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya musu daga bãyan tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini bã su haɗa kõme da Nĩ. Kuma wanda ya kãfirta a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai.
Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo, tsammãninku a yi muku rahama.
Kada lalle ka yi zaton waɗanda suka kãfirta zã su buwãya a cikin ƙasa, kuma makõmarsu wuta ce, kuma lalle ne makomar tã mũnana.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni* sau uku; daga gabãnin sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
____________________
* Ladabin shiga gida shĩ ne dukan yãron da ya balaga, ɗa ne kõ bãwa, kada ya shiga gida kõ a ɗãki a bãyan sallama sai ya nemi izni da cewa "In shiga?" Idan an karɓa masa da izni, ya shiga, idan kuma yanã zaton ba a ji shi ba, sai ya sãke neman izni har sau uku. neman izni yanã wajaba kõ ga yãran gidan a cikin lõkuta uku, wãtau a gabãnin sallar asuba da lõkacin tsakar rãnar na ƙailũla da bãyan sallar ishã'i.
Kuma idan yãra daga cikinku suka isa mafarki to su nẽmi izni, kamar yadda waɗanda suke a gabãninsu suka nẽmi iznin. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
Kuma tsõfaffi daga mãtã, waɗanda bã su fatan wani aure to, bãbu laifi a kansu su ajiye tufãfinsu, bã sunã mãsu fitar da ƙawa ba, kuma su tsare mutuncinsu shĩ ne mafi alhẽri a gare su. Kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.
Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku,* gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali.
____________________
   * Akwai daga ladubban zamantakewa har dai a tsakãnin dangi a ci abincin jũna, kõ aci tãre a waje guda, kõ kuwa kõwa ya ci dabam. Kuma idan an haɗu a yi gaisuwã a tsakãnin jũna, gaisuwa irin wadda Allah Ya ce Musulmi su yi wa jũnansu da cewa "Assalãmu alaikum". Ita ce gaisuwa mai kyau. Anã ƙãra "Wa rahmatul Lãhi wa barakãtuh," dõmin ta ƙãra dãɗi.
Waɗanda ke mũminai sõsai, su ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tãre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bã su tafiya sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke yin ĩmãni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabõda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmã musu gãfara daga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai*.
____________________
   * Babban ladabin haɗuwar jama'a shĩ ne ĩmãni da Allah kuma da ManzonSa. Sa'an nan kuma biyayya ga shũgaba wajen ayyukan gayya na rãyuwa haɗe, kamar ginin masallaci da hanya da kãsuwa da maƙabarta. Shũgaba yanã da ĩkon bãyar da iznin fakuwar mai uzuri, kuma yanã da ĩkon hanãwa gwargwadon hãli. Wannan kuma ya nũna muhimmancin aikin gayya da tsayuwar shũgaba a kansa, da wajabcin karɓa kira zuwa gare shi. Kuma wannan yanã nũna halaccin karɓar harãji daga mutãne dõmin a tsayu da bukãtocin haɗuwar jama'a gwargwadon hãli.
Kada ku sanya kiran Manzo* a tsakãninku kamar kiran sãshenku ga sãshe. Lalle ne Allah Yanã sanin waɗanda ke sancẽwa daga cikinku da saɗãɗe. To, waɗanda suke sãɓãwa daga umurninSa, su yi saunar wata fitina ta sãme su, kõ kuwa wata azãba mai raɗãɗi ta sãme su.
____________________
  * Wannan yanã nũna ladabin yadda ake kiran Manzon Allah tã hanya mai ladabi. Kada a kira shi da sũnansa kamar yadda ake kiran sauran mutãne da 'Yã Ali', 'Ya zaid,' sai dai a ce Yã Manzon Allah! a cikin sauti mai laushi mai dãɗi. Kuma wannan ladabi yanã shãfar dukan Musulmi na kõwane zãmani game da shũgabansu wanda yake shũgabantar su ga al'amurransu na zamantakewa. Kuma wannan yanã nũna rashin kyãwon mãsu cewa sunã zikiri da kiran sũnan Allah kamar haka "Allah! Allah! Allah!" Sabõda rashin ladabin da ke cikin yin haka ga Manzon Allah balle ga Allah.Ba a yin addini sai yadda Allah Yake son a yi Masa, wãtau yadda AnnabinSa ya shiryar da mutãne dõmin su bi Shi, su yi aiki da shi, Kuma sãɓã wa umurnin Annabi yanã sabbaba fitina ga mutãne kõ kuma ga ƙasa gabã ɗaya.
To! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa, Yanã sanin abin da kuke a kansa kuma a rãnar da ake mayar da su zuwa gare shi, sai Yanã bã su lãbãri game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kõme, Masani ne.