surah.translation .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

¦.H.
Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba.
Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah.
(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka.
Mai rahama, Ya daidaita* a kan Al'arshi.
____________________
 * Allah Ya daidaitu a kan Al'arshi daidaita wadda ta dãce da shi.
Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya.
Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa.
Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau.
Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka?
A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar."
Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!"
"Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka* Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa."
____________________
   * An ce wa Mũsã ya ɗebe takalmansa dõmin sunã da najasa kõ kuwa sũ kansu najasa ne dõmin ya shiga wuri mai tsarki wanda ake kira Ɗuwa a cikin sahãrar Sina'i a tsakãnin Masar da Madyana.".
"Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi."
"Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni."
"Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa."
"Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka."
"Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!"
Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci* na dabam a gare ta."
____________________
* Amfãnõnin sanda: Anã riƙon alkĩbla a cikin daji ta zama sitra, anã dõgara a kanta sabõda gajiya kõ rauni. Lĩmãmin Juma'a na dõgara a kanta a lõkacin huɗuba anã fita da ita a cikin ruwan sama anã dõgara a kanta, anã dũkan iyãli da ita dõmin ladabtarwa. A cikin wani Hadĩsi Annabi ya ce: "Ka rãtaye sandarka inda iyãlinka suke ganin ta." Riƙon sanda na sanya farkawa gabarin dũniya, watau mai ita ya zama a cikin hãlin tafiya.
Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!"
Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa.
Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko."
"Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam."
"Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyinMu manya."
"Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)."
Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa* mini, ƙirjĩna.
____________________
 * Ma'anar buɗa ƙirji, shine a sanya masa haƙuri.".
kuma ka sawwake mun Al'amari na
"Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna."
"Su fahimci maganãta."
"Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena."
"Hãrũna ɗan'uwana."
"Ka ƙarfafa halittata da shi."
"Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina."
"Dõmin mu tsarkake Ka da yawa."
"Kuma mu tuna Ka da yawa."
"Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu."
Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã!"
"Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam."
"A lõkacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka."
"Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a kan ganiNa."
"A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi* kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã Mũsã!
____________________
   * Idon ta ya yi sanyi, watau ta ji dãɗi sabõda ganin ɗanta.".
"Kuma Na zãɓe ka dõmin Kaina."
"Ka tafi kai da ɗan'uwanka game da ãyõyiNa, kuma kada ku yi rauni ga ambatõNa."
"Ku tafi kũ biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (ga girman kai)."
"Sai ku gaya masa magana mai laushi,* tsammãninsa yanã tunãwa kõ kuwa ya ji tsõro."
____________________
  * Wannan shĩ ne dalilin umurni da alheri da hani daga sharri, kuma a yi haka da maganamai laushi ga wanda yake da iko da ƙarfi. Kõ dã ga wanda Allah Ya tsare da tsarinsa ne, balle ga wanda bai tãki kõme ba. Ta haka ne mai wa'azi ke cin nasara.
Su biyu suka ce: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne munã tsõron ya yi gaggawa a kanmu, kõ ya ƙẽtare haddi."
Ya ce: "Kada ku ji tsõro. Lalle Nĩ, Inã tãre da ku, Inaji, kuma Inã gani."
"Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya."
"Lalle mũ, haƙĩƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cẽwaazãba tanã a kan wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya."
Ya ce: "To, wãne ne Ubangijinku? Ya Mũsã!"
Ya ce: "Ubangijinmu Shi ne wanda Ya bai wa dukan kõme halittarsa, sa'an nan Ya shiryar."
Ya ce: "To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko?"
Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa."
"Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi* Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam.
____________________
 * Ruwan.
Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali.
Daga gare ta* Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam.
____________________
 * Ƙasa.
Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyinMu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya!
Ya ce: "Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã?"
"To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa."
Ya ce: "Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi."
Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo.
Mũsã ya ce musu, "Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe."
Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãninsu kuma suka asirta gãnawa.
Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku* game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya."
____________________
 * Ya fara da siyãsa dõmin ya karkatar da hankalin mutãne daga ãyõyin Allah. Cewarsa yãyi nufin ya fitar da ku daga ƙasarku, shĩ ne siyãsa dõmin idan mutãne suka ji maganar fitarwa daga ƙasa, sai su manta da kõwace irin magana tawani alheri.
"Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta."
Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa."
Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri.
Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa.
Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka."
"Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je."
Sai aka jẽfar da masihirtan sunã mãsu sujada, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin Hãrũna da Mũsã."
Ya ce: "Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa, babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno, kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar (azãba)."
Suka ce: "Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa, ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne."
"Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kumaMafi wanzuwa."
Lalle* shĩ wanda ya je wa Ubangijinsa yanã mai laifi, to lalle ne yanã da Jahannama, bã ya mutuwa a cikinta kuma bã ya rãyuwa.
____________________
   * Ãyã ta 74 da ta 75 maganar Allah ce dõmin ƙarin bayãni a kan maganar masihirta a bãyan sun musulunta.
Kuma wanda ya je Masa yanã mai ĩmãni, alhãli kuwaya aikata aikin ƙwarai to waɗannan sunã da darajõji maɗaukaka.
Gidãjen Aljannar zama kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku.
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riskuwa, kuma bã ka fargabar nutsẽwa."
Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya rufe su.
Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar (dasu) ba.
Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku.
Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har hushĩNa ya sauka a kanku. Kuma wanda hushĩNa ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi.
Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa.
"Kuma mẽne ne ya gaggautar* da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã!"
____________________
   * Mũsã ya zãɓi mutun sabã'in daga Banĩ Isrã'ĩla, dõmin su tafi wurin Mĩƙãti tãre, su ji maganar Ubangiji. A lõkacin da ya yi kusa, sai ya yi gaggãwa dõmin bege. Kõ kuwa a bãyan azumin kwãna arba'in ya tafi a wurin Mĩƙãtin, Allah Ya fãra yi masa magana game da mutãnensa dõmin ɗebe masa kewa. Sai ya karɓa da cewa, "Sunã nan a kan sãwũna." Wãtau sunã nan a kan abin da na ɗõra su a kansa na addini da aƙĩda ta tauhĩdi. Sai Allah Ya ce masa "A'aha! sun musanya addininka da bautar maraƙi.".
Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda."
Ya ce: "To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su."
Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna?"
Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka* ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa."
____________________
  * Alõkacin da Banĩ Isrã'ĩla zãsu fita daga Masar sun yi aron mundãyen mutãnen Masar dõmin su nũna cewa biki suke yi, bã gudu zã su yi ba, dõmin kada a bĩ su da wuri waɗannan mundãyen ne sãmiri ya tãra a bãyan tafiyar Mũsã zuwa ga Mĩƙãtin Ubangijinsa ya ƙera musu maraƙi mai jiki irin na mutãne da sauti irin na shãnu dõmin yã yi masa magudãnar iska a cikin cikinsa idan iskar ta fito, sai a jĩ ta da sauti kamar sautin kũkan shãnu. Kuma shi maraƙin bã ya dã wani rai, bã ya mõtsi, sai dai ƙũgin kawai.
"Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta."
Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni?
Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umurnĩna."
Suka ce ba zamu gushe ba muna bauta a gareshi ba har sai Musa dawo
____________________
  * Lazimta a kan bautawa maraƙin akwai wahala a cikinta dõmin haka aka kãwo wannan ƙissa sabõda a nũna cewa bautar Allah bãbu lazimta da wahala a cikinta duk abin da yake da wahala a cikinsa, bã addinin Allah ba ne. Akwai ĩ'itikãfi a cikin Musulunci wanda mafi yawansa kwãna gõma ne a cikin masallaci. Mutãnen Sãmiri ne suka fãra ibãda da kiɗa da rawa da wãƙã a cikin wurin ibãdarsu.
(Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace."
"Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umurnina ne?"
(Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba."
(Mũsã) ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinka? Ya Sãmiri!"
(Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini."
(Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi,* sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa."
____________________
 * Mũsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya ƙõne maraƙin ya sheke shi a cikin ruwan teku ya nũna ĩkon maraƙin ga kãre kansa daga wata cũta kuma da ƙarancinsa a cikin teku wadda take ɗaya ce daga cikin abũbuwan ĩkon Allah da suke iya gani, da lãlãcewar ibãdar mãsu bauta wa wanin Allah, a bãyan wahalarsu mai yawa ta lazimta a kansa.
Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci* dukkan kõme da ilmi.
____________________
 * Allah Ya yalwaci dukan kõme da sani, watau Yanã aikata kõme da ilminsa kuma Yanã umurni da bauta Masa da ilmi, wanda Ya aiki Manzanninsa da shi.
Kamar wancan ne Muke lãbartãwa* a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gunMu.
____________________
   * Yã kãwo ƙãrin bayãni game da wannan ƙissa a cikin ãyõyin da ke tafe daga nan yadda bin addinin Allah yake da sauƙi a cikin lõkaci gajere na dũniya kawai a cikin taƙaitaccen lõkaci, da kuma wuyar bautawa wani ga ɗaukar kãya mãsu nauyi a dũniya da Lãhira, a cikin dõgon lõkaci.
Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanãɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma.
Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma.
A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu.
Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma."
Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda."
Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu* sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa,
____________________
   * Ana siffanta duwãtsu maɗaukaka da ayyukan dũniya waɗanda bã ibãdar Allah ba, watau al'adu da ibãdõjin da ba ibãdar Allah ba, dukansu kõme yawansu zã su lãlãce a rãnar da Mai kira, wãtau lsrãfĩl, zai bũsa ƙaho na kiran mutãne zuwa ga Tãshin Ƙiyãma, kira wanda bãbu makarkata daga gare shi, watau bã kamar kiran da Annabãwa suka yi ba, wanda waɗansu mutãne suka karkace daga gare shi a nan dũniya.
Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi.
"Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu."
A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya.
A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da magan*
____________________
   * Bãbu ceto ga kõwa sai wanda Allah Mai rahama Ya yi masa iznin da yin ceton, ga wanda aka yi iznin sabõda shi, kuma izni anã yin sa ne da maganar Allah, ba da wata ishãra ba.
Yanã sanin* abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani.
____________________
* Allah Ya san kõme ga halittunsa, su kuwa bã su iya kewayewa da sanin kõme game da shi.
Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye, Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe.
Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa.
Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa.
Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa* da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi."
____________________
   * Allah Ya umurci Annabi da ya bar gaggãwar karatun Alƙur'ãni a lõkacin da ake yin wahayinsa zuwa gare shi, dõmin kada ya wahala dõmin sũrar tanã karantar da cewa addinin Musulunci sauƙi ne, bai zo dõmin ya wahalar ba. Kuma tsõron yin kuskure yanã sanya yin kuskure mai jãwo wahala kamar yadda Ãdamu ya yi gaggãwar ga tsoron umurnin Allah, sai ya yi mantuwa, ya yi abin da aka hana shi har masifa ta sãmu aka fitar da shi daga Aljanna.
Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shiba.
Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada, fãce Iblĩsa, yã ƙiya.
Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi* ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala."
____________________
 * Anã farkar da ɗiyan Ãdamu ga maƙiyin ubansu wanda ya sabbaba musu wahalar zuwa dũniya da haɗuwa da taklĩfi a cikinta. Kuma bin wannan taklĩfi yanã zame masa sauƙi idan sun bĩ shi yadda Allah Ya ce: amma idan sun bi hanyar Shaiɗan, maƙiyinsu, to, bãbu abin da zai sãmu a gare su fãce ƙãrin wahala daga dũniya har Lãhira.
Lalle ne kã sãmu bã zã ka ji yunwa ba a cikinta, kuma bã zã ka yi tsiraici ba.
"Lalle kai, bã zã ka ji ƙishirwa ba, kuma bã zã ka shiga hantsi ba."
Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: "Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa?"
Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace.
Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi).
Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala."
"Kuma wanda ya bijire* daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho."
____________________
 * Wanda ya bijire daga ãyõyin Allah, shĩ ne kãfirin da bai yarda da shiga Musulunci ba.
Ya ce: "Ya Ubangiji! Don me Ka tãyar da ni makãho alhãli kuwa nã kasance mai gani?"
Ya ce: "Kamar wancan ne ãyõyinMu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka."
Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita,* kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa
____________________
   * Wanda ya yawaita, shi ne Musulmi fãsiƙi kõ mai bidi'a yanã ƙara abin da ba a sani ba a cikin addini, ya yawaita shi. Shi ma ya shiga a cikin wahalar dũniya. Kuma ta Lãhira ta fi tsanani.
Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda (kãfirai) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula.
Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta.
Sai ka yi haƙuri* a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda.
____________________
  * Haƙuri da riƙe ibãda ta sallõli da tasibĩhi a lõkutanta farilla da na nafila shi ne maganin izgilin mãsu izgili. Tasbĩhi da gõde wa Allah a gabanin fitõwar rãnã ga sallar Asuba, a gabanin ɓacewarta ga La'asar, a sã'õ'in dare ga Lisha, da gefukan rãna ga Azahar.
Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikinsa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa.
Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa.
Kuma suka ce: "Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa?" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba?
Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: "Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu!"
Ka ce: "Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa."