(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin* da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."— الترجمة الهوساوية
* Bãyin Allah sãlihai da malãiku waɗanda waɗansu mutãne suka bauta musu da tsammãnin cewa zã su cecesu daga Allah, bã zai sanya su Wuta ba sabõda ibãdar da aka yi musu, dõmin yabon Allah yã rigãyi hushinsa zuwa gare su. Bãyansu da mai bautar da wanda ake bautawar kamar gumãka da waɗansunsu, Wuta za su shiga.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationإِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمۡ لَهَا وَٰرِدُونَ(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."