Suna tambayar ka* ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai."— الترجمة الهوساوية
* Yã fãra Sũrar da tambayar Sahabbai ga Annabi cewa. wãne ne ya fi cancanta da dũkiyar ganĩmar da aka sãmu a yãƙin Badar Babba, samãri mayãƙa kõ tsõfaffi mãsu bãyar da shãwara da ra'ayõyinsu, mãsu kyau. Sa'annan ya yi jawãbi da cewa: "Ka ce ganimar ta Allah ce da ManzonSa," sabõda dalĩlan da suke tafe ga ayõyin da suke biye. Ana nufi wanke sõja daga jãyayya a kan dũkiya. AllahYa fi sani.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationAl'Anfal
يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَنفَالِۖ قُلِ ٱلۡأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَصۡلِحُواْ ذَاتَ بَيۡنِكُمۡۖ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَSuna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai."