Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: "Idan Allah Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."— الترجمة الهوساوية
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationيَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّمَن فِيٓ أَيۡدِيكُم مِّنَ ٱلۡأَسۡرَىٰٓ إِن يَعۡلَمِ ٱللَّهُ فِي قُلُوبِكُمۡ خَيۡرٗا يُؤۡتِكُمۡ خَيۡرٗا مِّمَّآ أُخِذَ مِنكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞYa kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: "Idan Allah Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."