Kuma ku ciyar* a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa.— الترجمة الهوساوية
* Bã a iya yãƙi sai da abinci, kuma bã kõwa ke iya zuwa yãƙi ba, kamar yadda yake bã kowa yake da abinci ba. Sabõda haka sai a ciyar da dũkiya, a tãra ta dõmin ɗaukaka kalmar Allah. Rashin bãyar da ita, to, halaka kai ne.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَأَنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا تُلۡقُواْ بِأَيۡدِيكُمۡ إِلَى ٱلتَّهۡلُكَةِ وَأَحۡسِنُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَKuma ku ciyar a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa.