Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da* Shi.— الترجمة الهوساوية
* Idan kanã son sanin siffofin Allah, sai ka tambayi Allah, dõmin bãbu wanda ya san shi, sani na gani balle ya iya gaya maka yadda Yake, sabõda haka siffõfin Allah da sũnãyenSa duka bã a yin shisshigi a gare su, sai yadda aka ji su daga Manzon Allah.Tauƙifiyyai ne.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ ٱلرَّحۡمَٰنُ فَسۡـَٔلۡ بِهِۦ خَبِيرٗاWanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da Shi.