Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare* da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa** wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.— الترجمة الهوساوية
* Isrã'i, shi ne tafiyar dare da Allah Ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitil Maƙadis. Sa'an nan Mi'iraji zuwa sama inda aka ba shi sallõli. ** Muƙarana a tsakãnin Masjidil Harãm watau tsararre daga a yãki mutãnensa da Masjidil Aƙsã wanda ba tsararre ba. Isrã'i da Mi'irãji sun fi Miƙãtin Mũsã da gãnãwarsa da Ubangiji a Ɗũr-Sĩna'a.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationAl-Isra'i
سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِيٓ أَسۡرَىٰ بِعَبۡدِهِۦ لَيۡلٗا مِّنَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ إِلَى ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡأَقۡصَا ٱلَّذِي بَٰرَكۡنَا حَوۡلَهُۥ لِنُرِيَهُۥ مِنۡ ءَايَٰتِنَآۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُTsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.