Ka ce: "Dã dai kũ, kunã mallakar* taskõkin rahamar Ubangijĩna, a lõkacin, haƙĩƙa dã kun kãme dõmin tsõron ƙãrẽwar taskõkin. Kuma mutum yã kasance mai ƙwauro ne."— الترجمة الهوساوية
* Muƙãrana a tsakãnin kyautar mutum da rõwarsa ga dũkiyar da ya mallaka.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationقُل لَّوۡ أَنتُمۡ تَمۡلِكُونَ خَزَآئِنَ رَحۡمَةِ رَبِّيٓ إِذٗا لَّأَمۡسَكۡتُمۡ خَشۡيَةَ ٱلۡإِنفَاقِۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ قَتُورٗاKa ce: "Dã dai kũ, kunã mallakar taskõkin rahamar Ubangijĩna, a lõkacin, haƙĩƙa dã kun kãme dõmin tsõron ƙãrẽwar taskõkin. Kuma mutum yã kasance mai ƙwauro ne."