Ka ce: "Ku yi ĩmãni* da Shi, ko kuwa kada ku yi ĩmãni, lalle ne waɗanda aka bai wa ilmi daga gabãninsa, idan anã karãtunsa a kansu, sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu, sunã mãsu sujada."— الترجمة الهوساوية
* Muƙãranar yin ĩmãni da rashin ĩmãnin mutãne ga Alƙur'ãni ba zai rage gaskiyarsa da kõme ba, sai dai waɗanda suka ƙi ĩmãnin ne zã su cũtu, sa'an nan da bambanci a tsakãnin mai ilmi da jãhili. Mai ilmi yanã da sauƙin jãwuwa zuwa ga gaskiya har ya rasa abin da zai aikata fãce ya fãɗi rikice, a kan haɓarsa, yanã mayar da al'amari ga Allah kuma yanã tawali'u.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationقُلۡ ءَامِنُواْ بِهِۦٓ أَوۡ لَا تُؤۡمِنُوٓاْۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ مِن قَبۡلِهِۦٓ إِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ يَخِرُّونَۤ لِلۡأَذۡقَانِۤ سُجَّدٗاۤKa ce: "Ku yi ĩmãni da Shi, ko kuwa kada ku yi ĩmãni, lalle ne waɗanda aka bai wa ilmi daga gabãninsa, idan anã karãtunsa a kansu, sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu, sunã mãsu sujada."