Kuma idan kuka sãka(7) wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri.— الترجمة الهوساوية
(7) Kuma mai kiran mutãne zuwa ga Allah lalle ne sai ya haɗu da cũtarwa daga mutãnen da bã su son gaskiyã. To, Allah bã Ya son zãlunci ko dã a kan maƙiyansa, sabõda haka Ya yi umurni da yin ƙisãsi da misãlin uƙũba, kõ a yi haƙuri, amma yin haƙuri yã fi rãmãwa dõmin nħman ni'imar Allah ta ƙãra kammala.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَإِنۡ عَاقَبۡتُمۡ فَعَاقِبُواْ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبۡتُم بِهِۦۖ وَلَئِن صَبَرۡتُمۡ لَهُوَ خَيۡرٞ لِّلصَّـٰبِرِينَKuma idan kuka sãka wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri.