(Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari,* Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."— الترجمة الهوساوية
* Wannan Gari shĩ ne Makka. Sanya Makka hurumi ba a iya shiga cikinsa da yãki yanã a cikin ashĩrai na Allah. Shiryuwa da ɓata duka asĩrai ne na Allah. Tsãrin Alƙur'ani da abubuwan da ya ƙunsa duka asĩran Allah ne.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationإِنَّمَآ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ رَبَّ هَٰذِهِ ٱلۡبَلۡدَةِ ٱلَّذِي حَرَّمَهَا وَلَهُۥ كُلُّ شَيۡءٖۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ(Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."