Kuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai,* haka kuma daga mutãnen Madnĩa. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su. zã Mu yi musu azãba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azãba mai girma.— الترجمة الهوساوية
* Kungiya ta biyu munãfukai mãsu zurfin wayo, sun san yadda suke ɓõye munãfuncinsu sabõda gõgewa da iya munãfunci har mutãne bã zã su iya gãne su ba, sai Allah Ya tõna su.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَمِمَّنۡ حَوۡلَكُم مِّنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مُنَٰفِقُونَۖ وَمِنۡ أَهۡلِ ٱلۡمَدِينَةِ مَرَدُواْ عَلَى ٱلنِّفَاقِ لَا تَعۡلَمُهُمۡۖ نَحۡنُ نَعۡلَمُهُمۡۚ سَنُعَذِّبُهُم مَّرَّتَيۡنِ ثُمَّ يُرَدُّونَ إِلَىٰ عَذَابٍ عَظِيمٖKuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai, haka kuma daga mutãnen Madnĩa. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su. zã Mu yi musu azãba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azãba mai girma.