Kuma da waɗansu waɗanda* aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.— الترجمة الهوساوية
* Wata ƙungiya wadda ita ba munãfuka ba ce, amma kuma ba su fita zuwa yãƙin ba, kuma bã su da wani dalĩli sai kasãla kawai da taushewar Shaiɗan. Waɗannan an jinkirtar da al'amarinsu har Allah Ya yi hukunci a kansu.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَءَاخَرُونَ مُرۡجَوۡنَ لِأَمۡرِ ٱللَّهِ إِمَّا يُعَذِّبُهُمۡ وَإِمَّا يَتُوبُ عَلَيۡهِمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞKuma da waɗansu waɗanda aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.