Shin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya* ni'imar Allah da kãfirci kuma suka saukar da mutãnensu a gidan halakã?— الترجمة الهوساوية
* Kuraishãwa wadanda Allah Ya yi musu ni'imar zama a cikin hurumin Allah da aminci da Ya zuba a kansu da albarku, sun musanya gõdiya da kãfirci a lõkacin da suka ƙaryata Manzon Allah. Sun saukar da mutãnensu a gidan halaka a Badar.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ بَدَّلُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ كُفۡرٗا وَأَحَلُّواْ قَوۡمَهُمۡ دَارَ ٱلۡبَوَارِShin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya ni'imar Allah da kãfirci kuma suka saukar da mutãnensu a gidan halakã?