Ka ce: "Wannan ce hanyãta;* inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba."— الترجمة الهوساوية
* Bin hukuncin Allah kamar yadda ƙissar Yũsufu ta nũna cewa, a ƙõwane hãli mutum ya kasance akwai yadda Allah Ya yi umurni a wannan hãlin da a bĩ Shi, wanda ya bi umurnin Allah, to, zai ɗaukaka a dũniya kuma Allah bã zai tõzartar da lãdarsa a Lãhira ba.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationقُلۡ هَٰذِهِۦ سَبِيلِيٓ أَدۡعُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِۚ عَلَىٰ بَصِيرَةٍ أَنَا۠ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِيۖ وَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَKa ce: "Wannan ce hanyãta; inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba."