ترجمة معاني سورة الطلاق باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Ya kai Annabi! Idan kun saki mãtã, sai ku sake su ga iddarsu,* kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãshã bayyananna. Kuma waɗancan iyakõkin Allah ne. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Ba ka sani ba ɗammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bãyan haka.
____________________
  * Saki, shĩ ne warware ƙullin halaccin sãduwa da jũna a tsakãnin miji da mãta. Haƙƙi ne wanda Allah Ya saka ga hannayen maza ban da mãtã. saki ga idda, watau ya sake ta saki gudã a cikin tsarkin dabai shãfe ta ba dõmin sauƙin idda. Yanã haramta ga mijin da mãtar ya fitar da ita kõ ta fita daga ɗãkinta a lõkacin idda. fãruwar wani al'amari shi ne sõyayya a bãyan ƙiyayya da mayarwa a bãyan saki. Alfãsha a nan, tanã nufin faɗa da zãge-zãge a kan surukantã. Anã fitar da mai iddar saki sabõda alfãsha daga gidanta.Akwai saki na sunna kuma akwai na bidi'a, amma saki na sunna ɗaya ne, a cikin tsarkin da bã a shãfe ta ba kuma kada a ƙãra mata wani saki har ta ƙãre idda, sakin bidi'a kuwa shĩne uku gabã ɗaya kõ a cikin idda gudã, a cikin haila kõ jinin bĩƙi. Sakin bidi'a yanã 1azimta, Anã tĩlastã shi mayarwa ga wadda aka saki a cikin haila idan bai kai uku ba ga miji 'yantacce, kõ biyu ga miji bãwã.
Sa'an nan idan sun isa ga ajalinsu (na idda) sai ku riƙe su da abin da aka sani kõ ku rabu da su da abin da aka sani kuma ku shaidar da mãsu adalci biyu daga gare ku. Kuma ku tsayar da shaidar dõmin Allah. Wancan ɗinku anã yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance yanã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita.
Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme.
Kuma waɗanda suka yanke* ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa.
____________________
* Muddar idda ga wadda ta yanke ɗammãnin haila, sabõda tsũfa, watanni uku,kuma bã zã ta ƙãra kõme ba a kai. Wadda take akwai shakka a game da ita ga kõ akwai ciki kõ bãbu shi, to, zã ta yi iddar wattani uku kuma ta yi jiran watanni tara, watau ta yi watannin shekara, uku na idda, saurãn na fidda shakkãne. Haka ne hukuncin mai istihãla, watau jinin ciwo. Amma yãrinya mai shakkar ciki, sai ta zauna har shakka ta gushe. Yarinyar da ba ta fãra haila ba tana iddar wata uku. Bãbu bambanci a tsakãnin ɗiya da baiwa ga idda da watanni, amma ga idda ta tsarki, to, baiwã tana yin rabin na ɗiya ga saki da mutuwa.
Wancan umurnin Allah ne, Ya saukar da shi zuwa gare ku. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sãkamako.
Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar* daga gwargwadon sãmunku. Kuma kada ku cũce su dõmin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abũta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shãyar da mãma sabõda ku, sai ku bã su tsãdõdinsu. Kuma ku yi shãwara a tsakãninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nũna talauci to wata mace zã ta shãyar da mãma sabõda shi (mijin).
____________________
 * Mijin zai fita ya bar wa mãtar da ya saki ɗaki ta zauna a ɗakinta har ta ƙãre idda. Anã ciyar da mai sakin kõme, amma bã a ciyar da mai sakin bã'ini sai idan tanã da ciki. Ijãrar shãyarwa tanã akan uba ga uwar da aka saki saki bã'ini kõ ga watarta, bisa ga yardar sassan biyu.
Sai mawadãci ya ciyar daga wadãtarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya bã shi. Allah bã Ya kallafa wa wani rai fãce abin da Ya bã shi. Allah zai sanya sauƙi a bãyan tsanani.
Kuma da yawa* daga alƙarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umurnin Ubangijinta da ManzanninSa, sai Muka yi mata hisãbi, hisãbi mai tsanani, kuma Muka, azabtar da ita azãba abar ƙyãma.
____________________
 * A bãyan da ya gama bayãnin saki da hukunce-hukuncen da suka rãtayu a gare shi, sai kuma ya gõya gargaɗi ga wanda bai bi waɗannan hukunce-hukuncen ba, ta hanyar tsoratar da shi da cewa Allah Ya halaka alƙaryu mãsu yawa sabõda sãɓã Masa ga hukunce-hukuncenSa ga ƙanãnan abũbuwa, balle mutum guda wanda ya sãɓã masa ga babban al'amari kamar aure da saki waɗanda rãyuwar ɗan Adam ta dõgara a kansu kuma ya yi bushãra ga wanda ya bĩ shi da taƙawa, ya fita daga duhun al'ãdu zuwa ga hasken sharĩ'arSa, kuma Ya yi wa'adi da bã shi sauƙin rãyuwa daga wadãtarSa mai yawa.
Sa'an nan ta ɗanɗana masĩfar al'amarinta. kuma ƙarshen al'amarinta ya kasance hasãra,
Allah Ya yi musu tattalin wata azãba mai tsanani. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abũta hankula, waɗanda suka yi ĩmãni! Haƙĩƙa Allah Ya saukar da wata tunãtarwa zuwa gare ku.
Manzo, yanã karãtun ãyõyin Allah bayyananu a kanku dõmin Ya fitar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidãjen Aljanna ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashnsu sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada. Haƙĩƙa Allah Yã kyautata* masa arziki.
____________________
 * Allah Yã kyautata wa wanda ya tsare sharĩ'arsa da kyau, awajen arzikinsa tun daga dũniya har ya zuwa Lãhira, dõmin Yã ce: "Haƙĩƙa Allah Yã kyautatã masa (mai tsare sharĩ'ar) arziki," bã da Yã yi ƙaidin lõkaci kõ wuri ba.
Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma daga ƙasã kwatankwacinsu, umuruinSa yanã ta sauka a tsakaninsu dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõme, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõme da sani.