وَلَا تَجۡعَلُواْ ٱللَّهَ عُرۡضَةࣰ لِّأَيۡمَٰنِكُمۡ أَن تَبَرُّواْ وَتَتَّقُواْ وَتُصۡلِحُواْ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمࣱ ٢٢٤
Al-Baqarah 2:224
سورة البقرة
Medinan
Verse: 224/286
Page 35
-
Hausa translation
الترجمة الهوساوية
Kuma kada ku sanya(5) Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.
(5) Bãyanin rantsuwa da hukunce-hukuncenta. Kada ku sanya rantsuwa da Allah sababin rashin aikata wani alheri, kõ wani aikin ɗã'a, kõ kuma sanya sulhu a tsakanin mutãne, kamar a rõƙe shi ga wani abu daga cikinsu, sai ya yi rantsuwa ya ce: "Wallãhi bã zan yi ba," dõmin tsare kansa daga aikatãwar abin da aka nema gare shi. Yin irin wannan rantsuwa makarũhi ne kõ haram, gwargwadon nauyin abin da aka yi ta sabõda rashin yin sa. Kambu shi ne wurin gwada harbi. -
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Kuma kada ku sanya Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.
Al-Baqarah 2:224
Loading the recitation…
0:00