وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولࣲ وَلَا نَبِيٍّ إِلَّآ إِذَا تَمَنَّىٰٓ أَلۡقَى ٱلشَّيۡطَٰنُ فِيٓ أُمۡنِيَّتِهِۦ فَيَنسَخُ ٱللَّهُ مَا يُلۡقِي ٱلشَّيۡطَٰنُ ثُمَّ يُحۡكِمُ ٱللَّهُ ءَايَٰتِهِۦۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمࣱ ٥٢
Al-Hajj 22:52
سورة الحج
Medinan
Verse: 52/78
Page 338
-
Hausa translation
الترجمة الهوساوية
Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri,* sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyinSa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
* Annabãwa sukan yi wahami ga tunãninsu, su yi zaton wani abu daidai ne alhãli kuwa a wurin Allah bã haka Yake nufi ba. A kan wannan, sai shakka ta shiga wãwã a kansu, amma wanda ke da ĩmãni to bã zai rikice ba sabõda wannan kuskure dõmin Allah bã Ya barin su a kansa, sai Ya gyãra abin da ke ciki na wahami. Misãli ƙissar Yũnusu, da ƙissar Annabi a cikin suratu Abasa, da ƙissar Ibrãhim wajen jãyayya da malã'ikun da aka aika zuwa alƙaryõyin mutãnen Lũɗu. -
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri, sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyinSa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
Al-Hajj 22:52
Loading the recitation…
0:00