قُل لَّوۡ كَانَ ٱلۡبَحۡرُ مِدَادࣰا لِّكَلِمَٰتِ رَبِّي لَنَفِدَ ٱلۡبَحۡرُ قَبۡلَ أَن تَنفَدَ كَلِمَٰتُ رَبِّي وَلَوۡ جِئۡنَا بِمِثۡلِهِۦ مَدَدࣰا ١٠٩
Al-Kahf 18:109
سورة الكهف
Meccan
Verse: 109/110
Page 304
-
Hausa translation
الترجمة الهوساوية
Ka ce: "Dã tẽku(6) ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari."
(6) Ma'anar ãyar nan ita ce Allah ne Mafi sani. llmin Allah bã shi da iyãka, kõ kalmõmin da suka ɗauki ma'anõninsa, bã zã a iya rubuta su ba, balle ma'anõnin da ke cikinsu. Sabõda haka abin da ke hankali a mutum, shĩ ne ya yi aiki da ɗan ilmin da Allah Ya umurce shi da aiki dashi. Idan ya nemi ya wuce nan, to, ya halakar da kansa dõmin bai san inda zai fãɗa ba. Wannan ilmin shi ne sharĩ'a da aiki da ita. -
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Ka ce: "Dã tẽku ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari."
Al-Kahf 18:109
Loading the recitation…
0:00