يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ هَمَّ قَوۡمٌ أَن يَبۡسُطُوٓاْ إِلَيۡكُمۡ أَيۡدِيَهُمۡ فَكَفَّ أَيۡدِيَهُمۡ عَنكُمۡۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ١١
Al-Ma'idah 5:11
سورة المائدة
Medinan
Verse: 11/120
Page 109
-
Hausa translation
الترجمة الهوساوية
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku* sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai.
* Wannan kiyãyewa ya auku a wurãre da yawa tun Musulmi suna da rauni kuma kãfirai suna da ƙarfi, kuma suna son su kashe Musulmi da Musulunci. Allah Ya tsare su. Saboda haka yanzu da Musulmi suka yi ƙarfi da ƙarfin Allah, yã wajaba a kansu su godewa Allah da taƙawa. Watau su riƙe alkawarin Allah, su yi abin da Ya aza musu gwargwadon hãli. -
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai.
Al-Ma'idah 5:11
Loading the recitation…
0:00