سَتَجِدُونَ ءَاخَرِينَ يُرِيدُونَ أَن يَأۡمَنُوكُمۡ وَيَأۡمَنُواْ قَوۡمَهُمۡ كُلَّ مَا رُدُّوٓاْ إِلَى ٱلۡفِتۡنَةِ أُرۡكِسُواْ فِيهَاۚ فَإِن لَّمۡ يَعۡتَزِلُوكُمۡ وَيُلۡقُوٓاْ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَمَ وَيَكُفُّوٓاْ أَيۡدِيَهُمۡ فَخُذُوهُمۡ وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ ثَقِفۡتُمُوهُمۡۚ وَأُوْلَٰٓئِكُمۡ جَعَلۡنَا لَكُمۡ عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنࣰا مُّبِينࣰا ٩١
An-Nisa' 4:91
سورة النساء
Medinan
Verse: 91/176
Page 92
-
Hausa translation
الترجمة الهوساوية
Za ku sãmi wasu* sunã nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutãnensu, kõ da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyã su a cikinta. To, idan ba su nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kãmã su, kuma ku kashe su inda duk kuka kãmã su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalĩli bayyanannea kansu.
* Sun bayyana ĩmãninsu gare ku dõmin ku amince musu, kuma sun bayyana kãfirci a wurin mutãnensu kãfirai domin su amince musu watau suna ido ruwa ido tudu. Sũ kam kãfirai ne, ku yãƙe su, sai fa idan sun musulunta, ko kuma sun bayyana sulhunsu sosai a gare ku. -
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Za ku sãmi wasu sunã nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutãnensu, kõ da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyã su a cikinta. To, idan ba su nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kãmã su, kuma ku kashe su inda duk kuka kãmã su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalĩli bayyanannea kansu.
An-Nisa' 4:91
Loading the recitation…
0:00