وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَشۡتَرِي لَهۡوَ ٱلۡحَدِيثِ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمࣲ وَيَتَّخِذَهَا هُزُوًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابࣱ مُّهِينࣱ ٦
Luqman 31:6
سورة لقمان
Meccan
Verse: 6/34
Page 411
-
Hausa translation
الترجمة الهوساوية
Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi* dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.
* Tatsũniyõyi sunã shagaltarwa daga ilmi mai sanya sanin Allah. Allah Ya hana a yi tarbiyyar yãra game da tãtsũniya mai ɗauke hankalinsu daga ibãda, Littattafan makaranta na zãmani da jarĩdu duka tãtsũniyõyi ne, sai abin da ya dãce da sunna. -
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.
Luqman 31:6
Loading the recitation…
0:00