At-Taubah 9:25

سورة التوبة

Medinan Verse: 25/129 Page 190

لَقَدۡ نَصَرَكُمُ ٱللَّهُ فِي مَوَاطِنَ كَثِيرَةࣲ وَيَوۡمَ حُنَيۡنٍ إِذۡ أَعۡجَبَتۡكُمۡ كَثۡرَتُكُمۡ فَلَمۡ تُغۡنِ عَنكُمۡ شَيۡـࣰٔا وَضَاقَتۡ عَلَيۡكُمُ ٱلۡأَرۡضُ بِمَا رَحُبَتۡ ثُمَّ وَلَّيۡتُم مُّدۡبِرِينَ ٢٥

  1. Hausa translation

    الترجمة الهوساوية

    Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a cikin wurãre mãsu yawa, da Rãnar Hunainu,* a lõkacin da yawanku ya bã ku sha'awa, sai bai amfãnar da ku da kõme ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka jũya kunã mãsu bãyar da bãya.
     * Hunainu wani wãdi ne a tsakãnin Makka da Ɗã'ifa inda Musulmi suka yi yãƙi da Hawãzinãwa, a cikin Shawwal shekara ta takwas. Yawan Musulmi ya rũɗe su har suka ce: "Yau bã zã a rinjãye mu ba, sabõda ƙaranci." Yawansu yã kasance dubũ gõma sha biyu, kuma kãfirai dubũ huɗu, sai suka ji tsõro, suka gudu, suka bar Annabi a kan alfadararsa Baidã'a, bãbu kõwa tãre da shĩ fãce Abbas da Abu Sufyãna wanda yake riƙe da likkãfar Annabi. Annabi ya sanya Abbas ya yi ta kiran su,"Yã Ansãr! Ya Mũhajirũn!" Har suka kõmo aka ci nasara.
  2. Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation


    Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a cikin wurãre mãsu yawa, da Rãnar Hunainu, a lõkacin da yawanku ya bã ku sha'awa, sai bai amfãnar da ku da kõme ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka jũya kunã mãsu bãyar da bãya.

Read the whole surah Arabic tafsir