فَقَالُواْ رَبَّنَا بَٰعِدۡ بَيۡنَ أَسۡفَارِنَا وَظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَحَادِيثَ وَمَزَّقۡنَٰهُمۡ كُلَّ مُمَزَّقٍۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتࣲ لِّكُلِّ صَبَّارࣲ شَكُورࣲ ١٩
Saba' 34:19
سورة سبأ
Meccan
Verse: 19/54
Page 430
-
Hausa translation
الترجمة الهوساوية
Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce* su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya.
* Muka sanya saba'ãwa suka wãtse a cikin waɗansu ƙasãshe sabõda ruwa ya halaka ƙasãrsu, sa'an nan kuma ta bũshe bãbu wadãta, har ana cewa 'Sun yi rarrabar Saba'ãwa' watau sun wãtse. -
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya.
Saba' 34:19
Loading the recitation…
0:00