سورة الأعلى

الترجمة الهوساوية

ترجمة معاني سورة الأعلى باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

آية رقم 2
Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
آية رقم 3
Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
آية رقم 5
Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
آية رقم 6
Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
آية رقم 8
Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
آية رقم 9
Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
آية رقم 11
Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
آية رقم 14
Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
آية رقم 15
Kuma ya ambaci sũnan(5) Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
  (5) Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran.
آية رقم 16
Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.*
  * Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira.
آية رقم 17
Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
آية رقم 18
Lalle ne, wannan* yanã a cikin littafan farko.
  * Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko.
تقدم القراءة