سورة سبأ

الترجمة الهوساوية

ترجمة معاني سورة سبأ باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Waɗancan suna da wata gãfara da wani arziki mai karimci.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin zã mu nũna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsãge ku, kõwace irin tsattsãgẽwa, lalle kũ, tabbas, kunã a cikin wata halitta sãbuwa.?"
Lalle, haƙĩƙa, akwai ãyã ga saba'ãwa* a cikin mazauninsu: gõnakin lambu biyu, dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gõdiya gare shi. Gari mai dãɗin zama, da Ubangiji Mai gãfara."
  * Ƙissar Dãwũda da ta Sulaimãn sunã nũna yadda Allah ke sauƙaƙe wa bãyinsa hanyar ibãda da ta sãmun abinci da sauƙi idan sun mayar da al'amuransu gare shi. Ƙissar sabaãwa tanã nũna yadda Allah ke karɓe wadãta daga wanda ya kãfirce Masa
Sai suka bijire sabõda haka Muka saki Mãlãlin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gõnakinsu biyu da waɗansu gõnaki biyu mãsu 'ya'yan itãce kaɗan: talãkiya da gõriba da wani abu na magarya kaɗan.
Wancan, da shi Muka yi musu sakamako sabõda kãfircinsu. Kuma lalle, bã Mu yi wa kõwa* irin wannan sakamako, fãce kafirai.
  * Allah na saka wa kãfirai gwargwadon aikinsu, kuma Yanã yin falala ga mũmini da kyautar da ta fi aikinsa.
Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin* garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu."
   * Tafiya a tsakãnin Yemen, ƙasar Saba'awa da Syria, watau Sham, ƙasã mai albarka, ƙasarAnnabãwa kuma ƙasa mai yawan ruwa da itãce.
Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce* su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya.
   * Muka sanya saba'ãwa suka wãtse a cikin waɗansu ƙasãshe sabõda ruwa ya halaka ƙasãrsu, sa'an nan kuma ta bũshe bãbu wadãta, har ana cewa 'Sun yi rarrabar Saba'ãwa' watau sun wãtse.
"Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurinSa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye* tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma,"
   * Bãbu wanda ya san lõkacin bãyar da izni ga yin ceto kõ wanda zã a bai wa iznin ya yi, kõ a yi masa, Sabõda haka mutãne a Lãhira na cikin tsõro har a lõkacin da aka koranye tsõron ta hanyar bãyar da izni ga ceto babba ga Annabi Muhammadu, sai mũminai su yi farin ciki su dinga tambayar jũna da cewa, "Menene Ubangijinku Ya ce?" waɗansu su ce, "Yã faɗi gaskiya' Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.".
Ka ce: "Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba."
Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba, kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba (na waɗansu littattafan sama)." Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa makangara (shũgabanni) "Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai."
Kuma maraunana suka ce wa makangara. "Ã'a, (ku tuna) mãkircin dare da na rãna a lõkacin da kuke umurnin mu da mu kãfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abõkan tãrayya." Kuma suka assirtar da nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyin waɗanda suka kãfirta. Lalle, bã zã a yi musu sakamako ba fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
آية رقم 35
Kuma suka ce: "Mũ ne mafiya yawa ga dũkiya da ɗiya, kuma mu ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba."
Kuma dũkiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙãmi fãce wanda, ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai. To, waɗannan sunã da sakamakon ninkawa sabõda abin da suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin bẽnãye.
Kuma waɗanda suke mãkirci a cikin ãyõyinMu, sunã nẽman gajiyarwa, waɗannan abin halartãwa ne a cikin azãba.
Kuma rãnar da Allah Ya ke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Ya ce wa Malã'iku, "Shin, waɗannan kũ ne suka kasance sunã bauta wa?"
Sabõda haka, a yau sãshenku bã ya mallakar wani amfãni ga wani sãshen, kuma bã ya mallakar wata cũta, kuma Munã cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wutã wadda "kuka kasance game da ita, kunã ƙaryatãwa."
Kuma waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata, alhãli kuwa ba su kai ushurin-ushurin abin da Muka bã su ba, sai suka ƙaryata ManzanniNa! To, yãya musũNa (ga maƙaryata) ya kasance?
تقدم القراءة