ترجمة سورة الفيل

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة الفيل باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa* ba?
____________________
  * An yi Yãƙin Gĩwa shekarar haihuwar Annabi tsakãnin halaka su da haihuwarsa kwãna hamsin. Bayan shekara arba'in Annabi ya fara karantar da mutane. Ya karantar da su cikin shekara ashirin da uku, sa'an nan ya ƙaura. Bayansa da shekara hamsin waanda suka bi shi suka cinye duniya. Wannan yana nuna cewa mutane ba su samun daraja sai da riƙon addini da ilimi.
Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?
Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?
Icon