Surah At-Taghabun in Hausa

سورة التغابن

Medinan Verses: 18 Juz 28 Page 556 Revelation order: 108

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ لَهُ ٱلۡمُلۡكُ وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءࣲ قَدِيرٌ ١

Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah. Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon yi ne.

هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ فَمِنكُمۡ كَافِرࣱ وَمِنكُم مُّؤۡمِنࣱۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ ٢

Shĩ ne wanda Ya halitta ku. Sa'an nan daga gare ku akwai kãfiri kuma daga gare ku akwai mũmini. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.

خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّ وَصَوَّرَكُمۡ فَأَحۡسَنَ صُوَرَكُمۡۖ وَإِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ ٣

Ya halitta sammai da ƙasã da abin da yake hakkinSa. Kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku. Kuma zuwa gare Shi makõma take.

يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَيَعۡلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعۡلِنُونَۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ ٤

Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasã. Kuma Yanã sanin abin da kuke bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.

أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ نَبَؤُاْ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَبۡلُ فَذَاقُواْ وَبَالَ أَمۡرِهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمࣱ ٥

Shin, babban lãbãri bai je muku ba na waɗanda suka kãfirta daga gabãni, sai suka ɗanɗani uƙũbar al'amarinsu kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi?

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُۥ كَانَت تَّأۡتِيهِمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَقَالُوٓاْ أَبَشَرࣱ يَهۡدُونَنَا فَكَفَرُواْ وَتَوَلَّواْۖ وَّٱسۡتَغۡنَى ٱللَّهُۚ وَٱللَّهُ غَنِيٌّ حَمِيدࣱ ٦

Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?" Sai suka kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah wadãtacce ne, Gõdadde.

زَعَمَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَن لَّن يُبۡعَثُواْۚ قُلۡ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتُبۡعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلۡتُمۡۚ وَذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرࣱ ٧

Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne."

فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱلنُّورِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلۡنَاۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرࣱ ٨

Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai labartawa ne.

يَوۡمَ يَجۡمَعُكُمۡ لِيَوۡمِ ٱلۡجَمۡعِۖ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلتَّغَابُنِۗ وَمَن يُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ وَيَعۡمَلۡ صَٰلِحࣰا يُكَفِّرۡ عَنۡهُ سَيِّـَٔاتِهِۦ وَيُدۡخِلۡهُ جَنَّٰتࣲ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدࣰاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ ٩

A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma.

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ ١٠

Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ayõyinMu, waɗannan sũne'yan wuta, sunã madawwama a cikinta. Kuma tir da makõma, ita.

مَآ أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَمَن يُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ يَهۡدِ قَلۡبَهُۥۚ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمࣱ ١١

Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne.

وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَۚ فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَإِنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ ١٢

Kuma ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo. Sa'an nan idan kun jũya bãya, to, abin sani kawai, akwai iyarwa bayyananna a kan ManzonMu.

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ١٣

Allah bãbu wani abin bauta wa fãce Shi. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara.

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ مِنۡ أَزۡوَٰجِكُمۡ وَأَوۡلَٰدِكُمۡ عَدُوࣰّا لَّكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُمۡۚ وَإِن تَعۡفُواْ وَتَصۡفَحُواْ وَتَغۡفِرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِيمٌ ١٤

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi* a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
* Maƙiyi, shĩ ne mai hana mutumin da yake ƙiyayya da shi wani alheri ya sadu da shi. Idan son dũkiya kõ mãta kõ ɗiya ya hana mutum yin sadaka kõ fita zuwa jihãdji, to dũkiyar da mãtan da ɗiyan sun zama maƙiyansa ke nan.

إِنَّمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَأَوۡلَٰدُكُمۡ فِتۡنَةࣱۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمࣱ ١٥

Dũkiyõyinku da ɗiyanku fitina* ɗai ne. Kuma Allah, a wurinSa akwai wani sakamako mai girma.
* Fitina, ita ce duk abin da zai cũci mutum ta hanyar da yake amincewa, cũtar ta dũniya ce kõ ta Lãhira. Cũtar Lãhira ta fi tsanani sabõda girman hasãrar da ke a cikinta.

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُمۡ وَٱسۡمَعُواْ وَأَطِيعُواْ وَأَنفِقُواْ خَيۡرࣰا لِّأَنفُسِكُمۡۗ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفۡسِهِۦ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ ١٦

Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.

إِن تُقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنࣰا يُضَٰعِفۡهُ لَكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ شَكُورٌ حَلِيمٌ ١٧

Idan kun bai wa Allah rance, rance mai kyau, (Allah) zai ninka shi a gare ku kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai yawan gõdiya ne, Mai haƙuri.

عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ ١٨

Shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwayi, Mai hikima.

Other translations of this surah

Tafsir of this surah in Arabic Hausa translation

Surahs

1 Al-Fatihah Al-Fatiha · 7 verses · Meccan Juz 1 · Revealed 5 الفاتحة 2 Al-Baqarah Al-Bakarah · 286 verses · Medinan Juz 1 · Revealed 87 البقرة 3 Al-Imran Al-Imaran · 200 verses · Medinan Juz 3 · Revealed 89 آل عمران 4 An-Nisa' An-Nisa'i · 176 verses · Medinan Juz 4 · Revealed 92 النساء 5 Al-Ma'idah 120 verses · Medinan Juz 6 · Revealed 112 المائدة 6 Al-An'am 165 verses · Meccan Juz 7 · Revealed 55 الأنعام 7 Al-A'raf Al-A'araf · 206 verses · Meccan Juz 8 · Revealed 39 الأعراف 8 Al-Anfal Al'Anfal · 75 verses · Medinan Juz 9 · Revealed 88 الأنفال 9 At-Taubah 129 verses · Medinan Juz 10 · Revealed 113 التوبة 10 Yunus 109 verses · Meccan Juz 11 · Revealed 51 يونس 11 Hood Hud · 123 verses · Meccan Juz 11 · Revealed 52 هود 12 Yusuf 111 verses · Meccan Juz 12 · Revealed 53 يوسف 13 Ar-Ra'd Ra'ad · 43 verses · Medinan Juz 13 · Revealed 96 الرعد 14 Ibrahim 52 verses · Meccan Juz 13 · Revealed 72 إبراهيم 15 Al-Hijr A-Hijr · 99 verses · Meccan Juz 14 · Revealed 54 الحجر 16 An-Nahl 128 verses · Meccan Juz 14 · Revealed 70 النحل 17 Al-Isra Al-Isra'i · 111 verses · Meccan Juz 15 · Revealed 50 الإسراء 18 Al-Kahf 110 verses · Meccan Juz 15 · Revealed 69 الكهف 19 Maryam Marya · 98 verses · Meccan Juz 16 · Revealed 44 مريم 20 Ta­Ha Taha · 135 verses · Meccan Juz 16 · Revealed 45 طه 21 Al-Anbiya' Al-Anbiya · 112 verses · Meccan Juz 17 · Revealed 73 الأنبياء 22 Al-Hajj 78 verses · Medinan Juz 17 · Revealed 103 الحج 23 Al-Mu'minun Al-Muminu · 118 verses · Meccan Juz 18 · Revealed 74 المؤمنون 24 An-Nur 64 verses · Medinan Juz 18 · Revealed 102 النور 25 Al-Furqan Al-Furkan · 77 verses · Meccan Juz 18 · Revealed 42 الفرقان 26 Ash-Shu'ara' As-Shu'ara · 227 verses · Meccan Juz 19 · Revealed 47 الشعراء 27 An-Naml 93 verses · Meccan Juz 19 · Revealed 48 النمل 28 Al-Qasas Al-Kasas · 88 verses · Meccan Juz 20 · Revealed 49 القصص 29 Al-'Ankabut Al-Ankabut · 69 verses · Meccan Juz 20 · Revealed 85 العنكبوت 30 Ar­Room Ar-Rum · 60 verses · Meccan Juz 21 · Revealed 84 الروم 31 Luqman Lukuman · 34 verses · Meccan Juz 21 · Revealed 57 لقمان 32 As­Sajdah As-Sajadah · 30 verses · Meccan Juz 21 · Revealed 75 السجدة 33 Al­Ahzab Al-Ahzab · 73 verses · Medinan Juz 21 · Revealed 90 الأحزاب 34 Saba' Saba'i · 54 verses · Meccan Juz 22 · Revealed 58 سبأ 35 Fatir 45 verses · Meccan Juz 22 · Revealed 43 فاطر 36 Ya­Sin Yasin · 83 verses · Meccan Juz 22 · Revealed 41 يس 37 As-Saffat 182 verses · Meccan Juz 23 · Revealed 56 الصافات 38 Sad 88 verses · Meccan Juz 23 · Revealed 38 ص 39 Az-Zumar 75 verses · Meccan Juz 23 · Revealed 59 الزمر 40 Ghafir 85 verses · Meccan Juz 24 · Revealed 60 غافر 41 Fussilat 54 verses · Meccan Juz 24 · Revealed 61 فصلت 42 Ash-Shura As-Shurah · 53 verses · Meccan Juz 25 · Revealed 62 الشورى 43 Az-Zukhruf 89 verses · Meccan Juz 25 · Revealed 63 الزخرف 44 Ad-Dukhan 59 verses · Meccan Juz 25 · Revealed 64 الدخان 45 Al-Jathiya Al-Jasiyah · 37 verses · Meccan Juz 25 · Revealed 65 الجاثية 46 Al-Ahqaf Al-Ahkaf · 35 verses · Meccan Juz 26 · Revealed 66 الأحقاف 47 Muhammad 38 verses · Medinan Juz 26 · Revealed 96 محمد 48 Al-Fath 29 verses · Medinan Juz 26 · Revealed 111 الفتح 49 Al-Hujurat 18 verses · Medinan Juz 26 · Revealed 106 الحجرات 50 Qaf Kaaf · 45 verses · Meccan Juz 26 · Revealed 34 ق 51 Az-Zariyat 60 verses · Meccan Juz 26 · Revealed 67 الذاريات 52 At-Tur 49 verses · Meccan Juz 27 · Revealed 76 الطور 53 An-Najm 62 verses · Meccan Juz 27 · Revealed 23 النجم 54 Al-Qamar Al-Kamar · 55 verses · Meccan Juz 27 · Revealed 37 القمر 55 Ar-Rahman 78 verses · Medinan Juz 27 · Revealed 97 الرحمن 56 Al-Waqi'ah Al-Waki'ah · 96 verses · Meccan Juz 27 · Revealed 46 الواقعة 57 Al-Hadid AlHadid · 29 verses · Medinan Juz 27 · Revealed 94 الحديد 58 Al-Mujadilah Al-Mujadalah · 22 verses · Medinan Juz 28 · Revealed 105 المجادلة 59 Al-Hashr 24 verses · Medinan Juz 28 · Revealed 101 الحشر 60 Al-Mumtahinah Al-Mumtahanah · 13 verses · Medinan Juz 28 · Revealed 91 الممتحنة 61 As-Saff 14 verses · Medinan Juz 28 · Revealed 109 الصف 62 Al-Jumu'ah Al-Juma'ah · 11 verses · Medinan Juz 28 · Revealed 110 الجمعة 63 Al-Munafiqun Al-Munafikun · 11 verses · Medinan Juz 28 · Revealed 104 المنافقون 64 At-Taghabun 18 verses · Medinan Juz 28 · Revealed 108 التغابن 65 At-Talaq At-Talak · 12 verses · Medinan Juz 28 · Revealed 99 الطلاق 66 At-Tahrim 12 verses · Medinan Juz 28 · Revealed 107 التحريم 67 Al-Mulk 30 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 77 الملك 68 Al-Qalam Al-Kalam · 52 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 2 القلم 69 Al-Haqqah Al-Hakkah · 52 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 87 الحاقة 70 Al-Ma'arij 44 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 79 المعارج 71 Nooh Nouh · 28 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 71 نوح 72 Al-Jinn 28 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 40 الجن 73 Al-Muzzammil 20 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 3 المزمل 74 Al-Muddaththir Al-Muddasir · 56 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 4 المدثر 75 Al-Qiyamah Al-Kiyama · 40 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 31 القيامة 76 Al-Insan 31 verses · Medinan Juz 29 · Revealed 98 الإنسان 77 Al-Mursalat 50 verses · Meccan Juz 29 · Revealed 33 المرسلات 78 An-Naba' An-Naba'i · 40 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 80 النبأ 79 An-Nazi'at 46 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 81 النازعات 80 'Abasa Abasa · 42 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 24 عبس 81 At-Takwir An-Takwir · 29 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 7 التكوير 82 Al-Infitar 19 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 82 الإنفطار 83 Al-Mutaffifin 36 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 86 المطففين 84 Al-Inshiqaq Al-Inshikak · 25 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 83 الإنشقاق 85 Al-Buruj 22 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 27 البروج 86 At-Tariq At-Tarik · 17 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 36 الطارق 87 Al-A'la Al'A'alah · 19 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 8 الأعلى 88 Al-Ghashiyah 26 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 68 الغاشية 89 Al-Fajr 30 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 10 الفجر 90 Al-Balad 20 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 35 البلد 91 Ash-Shams As-Shams · 15 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 26 الشمس 92 Al-Lail 21 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 9 الليل 93 Ad-Duha Ad-Dhuhah · 11 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 11 الضحى 94 Ash-Sharh As-Sarhi · 8 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 12 الشرح 95 At-Tin 8 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 28 التين 96 Al-'Alaq Al'Alak · 19 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 1 العلق 97 Al-Qadr Al-Kadr · 5 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 25 القدر 98 Al-Baiyinah Al-Bayyinah · 8 verses · Medinan Juz 30 · Revealed 100 البينة 99 Az-Zalzalah Al-zalzalah · 8 verses · Medinan Juz 30 · Revealed 93 الزلزلة 100 Al-'Adiyat Al-Adiyat · 11 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 14 العاديات 101 Al-Qari'ah Al-Kari'ah · 11 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 30 القارعة 102 At-Takathur At-Takasur · 8 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 16 التكاثر 103 Al-'Asr Al'asri · 3 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 13 العصر 104 Al-Humazah Ali-Humazah · 9 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 32 الهمزة 105 Al-Fil 5 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 19 الفيل 106 Quraish Kuraish · 4 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 29 قريش 107 Al-Ma'un 7 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 17 الماعون 108 Al-Kauthar Al-Kausar · 3 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 15 الكوثر 109 Al-Kafirun 6 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 18 الكافرون 110 An-Nasr 3 verses · Medinan Juz 30 · Revealed 114 النصر 111 Al-Masad 5 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 6 المسد 112 Al-Ikhlas 4 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 22 الإخلاص 113 Al-Falaq Al-Flak · 5 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 20 الفلق 114 An-Nas 6 verses · Meccan Juz 30 · Revealed 21 الناس

Reading settings

View
Compare with

Pick up to two more translations to show under each verse.

Arabic size
100%
Translation size
100%
Line spacing
Theme

Verse

Verse page Arabic tafsir
Highlight

Highlights stay in this browser and are listed on the bookmarks page. /bookmarks