Surah Al-'Alaq in Hausa
Al'Alak · سورة العلق · Verses: 19 · Meccan
Translation: Hausa translation 1 (الترجمة الهوساوية)
-
1
ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِي خَلَقَ
Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta. -
2
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِنۡ عَلَقٍ
Ya hahitta mutum daga gudan jini. -
3
ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ
Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci. -
4
ٱلَّذِي عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ
Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami. -
5
عَلَّمَ ٱلۡإِنسَٰنَ مَا لَمۡ يَعۡلَمۡ
Ya sanar da mutum abin da bai sani ba. -
6
كَلَّآ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَيَطۡغَىٰٓ
A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu). -
7
أَن رَّءَاهُ ٱسۡتَغۡنَىٰٓ
Dõmin yã ga kansa, yã wadãta. -
8
إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجۡعَىٰٓ
Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take. -
9
أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يَنۡهَىٰ
Shin, kã ga wanda ke hana. -
10
عَبۡدًا إِذَا صَلَّىٰٓ
Bãwã idan yã yi salla? -
11
أَرَءَيۡتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلۡهُدَىٰٓ
Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya? -
12
أَوۡ أَمَرَ بِٱلتَّقۡوَىٰٓ
Ko ya yi umurni da taƙawa? -
13
أَرَءَيۡتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ
Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya? -
14
أَلَمۡ يَعۡلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ
Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani? -
15
كَلَّا لَئِن لَّمۡ يَنتَهِ لَنَسۡفَعَۢا بِٱلنَّاصِيَةِ
A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa. -
16
نَاصِيَةࣲ كَٰذِبَةٍ خَاطِئَةࣲ
Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi. -
17
فَلۡيَدۡعُ نَادِيَهُۥ
Sai ya kirayi ƙungiyarsa. -
18
سَنَدۡعُ ٱلزَّبَانِيَةَ
Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma). -
19
كَلَّا لَا تُطِعۡهُ وَٱسۡجُدۡۤ وَٱقۡتَرِب۩
A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).
* Wato salla da sauran ibãdu.