Surah At-Tin in Hausa
سورة التين · Verses: 8 · Meccan
Translation: Hausa translation 1 (الترجمة الهوساوية)
-
1
وَٱلتِّينِ وَٱلزَّيۡتُونِ
Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.*
* Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'. -
2
وَطُورِ سِينِينَ
Da Dũr Sĩnĩna.*
* Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa. -
3
وَهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ ٱلۡأَمِينِ
Da wannan gari* amintacce.
* Gari amintacce shi ne Makkah. -
4
لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِيٓ أَحۡسَنِ تَقۡوِيمࣲ
Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa. -
5
ثُمَّ رَدَدۡنَٰهُ أَسۡفَلَ سَٰفِلِينَ
Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni -
6
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَلَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونࣲ
Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa. -
7
فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعۡدُ بِٱلدِّينِ
To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)? -
8
أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَحۡكَمِ ٱلۡحَٰكِمِينَ
Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?*
* Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce بلى ,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci.