Surah Ad-Duha in Hausa
Ad-Dhuhah · سورة الضحى · Verses: 11 · Meccan
Translation: Hausa translation 1 (الترجمة الهوساوية)
-
1
وَٱلضُّحَىٰ
Inã rantsuwa da hantsi. -
2
وَٱلَّيۡلِ إِذَا سَجَىٰ
Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa). -
3
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ
Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba. -
4
وَلَلۡأٓخِرَةُ خَيۡرࣱ لَّكَ مِنَ ٱلۡأُولَىٰ
Kuma lalle ta ƙarshe* ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
* Ta ƙarshe, wãto, Lãhira; kuma ta farko, wato, dũniya. -
5
وَلَسَوۡفَ يُعۡطِيكَ رَبُّكَ فَتَرۡضَىٰٓ
Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda. -
6
أَلَمۡ يَجِدۡكَ يَتِيمࣰا فَـَٔاوَىٰ
Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma? -
7
وَوَجَدَكَ ضَآلࣰّا فَهَدَىٰ
Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai? -
8
وَوَجَدَكَ عَآئِلࣰا فَأَغۡنَىٰ
Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka? -
9
فَأَمَّا ٱلۡيَتِيمَ فَلَا تَقۡهَرۡ
Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi. -
10
وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنۡهَرۡ
Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa. -
11
وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ
Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).