Surah Al-Lail in Hausa
سورة الليل · Verses: 21 · Meccan
Translation: Hausa translation 1 (الترجمة الهوساوية)
-
1
وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰ
Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa. -
2
وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ
Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa. -
3
وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ
Da abin da ya halitta namiji da mace. -
4
إِنَّ سَعۡيَكُمۡ لَشَتَّىٰ
Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke. -
5
فَأَمَّا مَنۡ أَعۡطَىٰ وَٱتَّقَىٰ
To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa. -
6
وَصَدَّقَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ
Kuma ya gaskata kalma* mai kyãwo.
* Kalma mai kyãwo ita ce Kalmar shahãda da abin da ta ƙunsa na addinin Musulunci, wanda yake yinsa kamar yadda Allah Ya ce, ta hanyan ManzonSa, shi ne taƙawa. -
7
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡيُسۡرَىٰ
To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi. -
8
وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسۡتَغۡنَىٰ
Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa. -
9
وَكَذَّبَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ
Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo. -
10
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡعُسۡرَىٰ
To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani. -
11
وَمَا يُغۡنِي عَنۡهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ
Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta). -
12
إِنَّ عَلَيۡنَا لَلۡهُدَىٰ
Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya. -
13
وَإِنَّ لَنَا لَلۡأٓخِرَةَ وَٱلۡأُولَىٰ
Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne. -
14
فَأَنذَرۡتُكُمۡ نَارࣰا تَلَظَّىٰ
Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka. -
15
لَا يَصۡلَىٰهَآ إِلَّا ٱلۡأَشۡقَى
Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa -
16
ٱلَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya. -
17
وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلۡأَتۡقَى
Kuma mafi taƙawa* zai nisance ta.
* Mafi taƙawa da Mafi shaƙãwa suna ma'anar mai taƙawa da shaƙiyyi. -
18
ٱلَّذِي يُؤۡتِي مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ
Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka. -
19
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعۡمَةࣲ تُجۡزَىٰٓ
Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta. -
20
إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka. -
21
وَلَسَوۡفَ يَرۡضَىٰ
To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).