Surah Al-Mutaffifin in Hausa
سورة المطففين · Verses: 36 · Meccan
Translation: Hausa translation 1 (الترجمة الهوساوية)
-
1
وَيۡلࣱ لِّلۡمُطَفِّفِينَ
Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa. -
2
ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكۡتَالُواْ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسۡتَوۡفُونَ
Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu. -
3
وَإِذَا كَالُوهُمۡ أَو وَّزَنُوهُمۡ يُخۡسِرُونَ
Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikẽli, suna ragẽwa
* Mũdu. -
4
أَلَا يَظُنُّ أُوْلَٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبۡعُوثُونَ
Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba? -
5
لِيَوۡمٍ عَظِيمࣲ
Domin yini mai girma. -
6
يَوۡمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta? -
7
كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡفُجَّارِ لَفِي سِجِّينࣲ
Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn. -
8
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سِجِّينࣱ
Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn? -
9
كِتَٰبࣱ مَّرۡقُومࣱ
Wani ittãfi ne rubũtacce. -
10
وَيۡلࣱ يَوۡمَئِذࣲ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa. -
11
ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ
Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako. -
12
وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعۡتَدٍ أَثِيمٍ
Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi. -
13
إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne. -
14
كَلَّاۖ بَلۡۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu. -
15
كَلَّآ إِنَّهُمۡ عَن رَّبِّهِمۡ يَوۡمَئِذࣲ لَّمَحۡجُوبُونَ
A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne. -
16
ثُمَّ إِنَّهُمۡ لَصَالُواْ ٱلۡجَحِيمِ
Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne. -
17
ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi." -
18
كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡأَبۡرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ
A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna? -
19
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ
Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna? -
20
كِتَٰبࣱ مَّرۡقُومࣱ
Wani littãfi ne rubũtacce. -
21
يَشۡهَدُهُ ٱلۡمُقَرَّبُونَ
Muƙarrabai* suke halarta shi.
* Malã'iku masu daraja. -
22
إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٍ
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima. -
23
عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ
A kan karagu, suna ta kallo. -
24
تَعۡرِفُ فِي وُجُوهِهِمۡ نَضۡرَةَ ٱلنَّعِيمِ
Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima. -
25
يُسۡقَوۡنَ مِن رَّحِيقࣲ مَّخۡتُومٍ
Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta. -
26
خِتَٰمُهُۥ مِسۡكࣱۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلۡيَتَنَافَسِ ٱلۡمُتَنَٰفِسُونَ
¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma. -
27
وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسۡنِيمٍ
Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake. -
28
عَيۡنࣰا يَشۡرَبُ بِهَا ٱلۡمُقَرَّبُونَ
(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi. -
29
إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْ كَانُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَضۡحَكُونَ
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya. -
30
وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمۡ يَتَغَامَزُونَ
Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe. -
31
وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓاْ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمُ ٱنقَلَبُواْ فَكِهِينَ
Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci. -
32
وَإِذَا رَأَوۡهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ
Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne." -
33
وَمَآ أُرۡسِلُواْ عَلَيۡهِمۡ حَٰفِظِينَ
Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu. -
34
فَٱلۡيَوۡمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنَ ٱلۡكُفَّارِ يَضۡحَكُونَ
To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya. -
35
عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ
A kan karagu, suna ta kallo. -
36
هَلۡ ثُوِّبَ ٱلۡكُفَّارُ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ
Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?*
* Amsar tambaya "na'am.".