Surah Al-A'la in Hausa
Al'A'alah · سورة الأعلى · Verses: 19 · Meccan
Translation: Hausa translation 1 (الترجمة الهوساوية)
-
1
سَبِّحِ ٱسۡمَ رَبِّكَ ٱلۡأَعۡلَى
Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka. -
2
ٱلَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ
Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar. -
3
وَٱلَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ
Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri). -
4
وَٱلَّذِيٓ أَخۡرَجَ ٱلۡمَرۡعَىٰ
Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã. -
5
فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحۡوَىٰ
Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa. -
6
سَنُقۡرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ
Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba. -
7
إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ وَمَا يَخۡفَىٰ
Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye. -
8
وَنُيَسِّرُكَ لِلۡيُسۡرَىٰ
Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi. -
9
فَذَكِّرۡ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكۡرَىٰ
Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni. -
10
سَيَذَّكَّرُ مَن يَخۡشَىٰ
Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna. -
11
وَيَتَجَنَّبُهَا ٱلۡأَشۡقَى
Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta, -
12
ٱلَّذِي يَصۡلَى ٱلنَّارَ ٱلۡكُبۡرَىٰ
Wanda zai shiga wutar da tã fi girma. -
13
ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحۡيَىٰ
Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba. -
14
قَدۡ أَفۡلَحَ مَن تَزَكَّىٰ
Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo. -
15
وَذَكَرَ ٱسۡمَ رَبِّهِۦ فَصَلَّىٰ
Kuma ya ambaci sũnan(5) Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
(5) Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran. -
16
بَلۡ تُؤۡثِرُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا
Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.*
* Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira. -
17
وَٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرࣱ وَأَبۡقَىٰٓ
Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa. -
18
إِنَّ هَٰذَا لَفِي ٱلصُّحُفِ ٱلۡأُولَىٰ
Lalle ne, wannan* yanã a cikin littafan farko.
* Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko. -
19
صُحُفِ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ
Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.