ترجمة معاني سورة الماعون
 باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation
            .
            
                            
            
    ﰡ
Al-Ma'un
Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
To, wannan shi ne ke tunkue marãya (daga haƙƙinsa).
Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.
                                                                                                                
                                    ﭶﭷ
                                    ﰃ
                                                                        
                    To, bone yã tabbata ga masallata.
Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu.
Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu)
                                                                                                                
                                    ﮃﮄ
                                    ﰆ
                                                                        
                    Kuma suna hana taimako.