ترجمة معاني سورة الأحقاف باللغة الهوساوية من كتاب Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation

Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation

آية رقم 1

Al-Ahkaf


Ḥ. M̃.

Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi (da shi).

Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni: "Da (Alƙur'ãni) ya kasance, wani alhẽri ne," dã ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su shiryu game da shĩ ba, to, zã su ce, "Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe."

Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma rahama. Kuma wannan (Alƙur'ãni) littafi ne mai gaskatãwa (ga littafin Mũsã), a harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra ga mãsu kyautatãwa.

Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in, ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)."

Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: "Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni cẽwa zã a fitar da ni daga (kabari) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa sun shũɗe a gabãnĩna (ba su kõmo ba)?" Kuma sũ (mahaifan) sunã nẽman Allah taimako (sunãce masa) "Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa'adin Allah gaskiya ne." Sai shi kuma ya ce. "Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."

Kuma ga kõwane nau'i, yanã da darajõji daga abinda suka aikata. Kuma dõmin (Allah) Ya cika musu (sakamakon) ayyukansu, alhãli kuwa sũ, bã zã a zãlunce su ba.

Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã (a ce musu): "Kun tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi."

Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."

Kuma ne, lalle haƙĩƙa, Mun halakar da abin da yake kẽwayenku na alƙaryu kuma Muka jujjũya ãyõyi, tsammãninsu zã su kõmo.

Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi.

Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, (a ce musu) "Ashe, wannan bã gaskiya ba ne?" Su ce: "Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!" Sai Ya ce, "To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."
تقدم القراءة