ترجمة سورة التين

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة التين باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.*
____________________
* Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'.
Da Dũr Sĩnĩna.*
____________________
* Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa.
Da wannan gari* amintacce.
____________________
 * Gari amintacce shi ne Makkah.
Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?*
____________________
 * Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce بلى ,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci.
Icon