ترجمة سورة القصص

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة القصص باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

¦. S̃. M̃.
Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna.
Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda.
Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su.
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi, kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni
Sai mutãnen Fir'auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci.
Kuma matar* Fir'auna ta ce ("Ka bar shi yanã) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, kõ mu riƙe Shi ɗã," alhãli kuwa sũ ba su sansance ba.
____________________
  * Sunan mãtar Fir'auna Ãsiya, tanã da zumunta da Mũsã. Tace ka yi masa sũna 'Mũshã,' ma'anarsa an same shi tsakãnin "mũ," wãtau ruwa da "shã" watau itãce, sa'an nan ya zama Mũsã. Allah Yanã tsare mutum gaba ga maƙiyinsa.
Kuma zuciyar uwar Mũsã ta wãyi gari yõfintatta.* Lalle ne, haƙĩƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, bã dõmin Mun ɗaure zũciyarta ba, dõmin ta kasance daga mũminai.
____________________
   * Zũciya yõfintatta, ita ce wadda bã ta da wani tunãni sabõda abin da ya shagaltar da ita na tunãnin ɗanta a hannun maƙiyinsa.
Kuma ta ce wa 'yar'uwarsa,* "Ki bĩ shi." Sabõda haka sai ta lẽƙe shi daga gẽfe, alhãli sũ ba Su sani ba.
____________________
  * Sũnan 'yar'uwar Mũsã Maryamu ko Kalsuma ko Kalsumu. Sũnan uwarsu Yũhãniz ɗiyar Hãmid ɗan Lãwaya ɗan Yãƙũbu.
Kuma Muka hana masa mãsu shãyai da mãma, a gabãnin haka sai ta ce: "Kõ in nũnamuku mutãnen wani gida, su yi muku renonsa alhãli kuwa su mãsu nasĩha ne a, gare shi?"
Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa dõmin idanunta su yi sanyi, kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba, kuma dõmin ta san cẽwa lalle wa'adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
Kuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci* da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
____________________
  * Wannan ya nũna, cewa Mũsã an bã shi Annabci a gabãnin ya yi hijira zuwa Madyana. Kuma yanã ƙãra ƙarfafa wannan magana abin da ke cikin ãyã ta 16 inda ya rõƙi Allah gãfara, Ya gãfarta masa, da ãyã ta l7 wadda ta nũna ya san an yi masa gãfarar har yanã neman tsari dõmin kada ya kõma yin haka a gaba. Annabãwa sunã wahami ga abin da bã wahayi ba, sa'an nan Allah Ya gyãra kuskuren, Ya tabbatar da gaskiya.
Kuma sai ya shiga garin a lõkacin da mutãnen garin suka shagala, sai ya sãmu, a cikin garin, waɗansu maza biyu sunã faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa, sai Mũsã ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: "Wannan aikin Shaiɗan ne, dõmin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne!"
Ya ce: "Ya Uhangijĩna! Lalle na zãlunci kaina, sai Ka yi mini gãfara." Sai Ya gãfarta masa, dõmin Shĩ ne Mai yawan gãfara, Mai jin ƙai.
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Dõmin abin da Ka ni'imta shi a kaina, sahõda haka bã zan kasance mai taimako ga mãsu laifi ba."
Sai ya wãyi gari a cikin birnin yanã mai tsõro, yanã sauna. Sai ga wanda ya nẽmi taimako daga gare shi a jiya, yanã nẽman ãgajinsa. Mũsã ya ce masa, "Lalle kai ɓatacce ne, bayyananne."
To, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce,* "Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa** a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa."
____________________
 * Ya faɗi haka zaton Mũsã zai kashe shi ne sabõda gargaɗin da ya gabãtar a gareshi, Maganar ta nũna Mũsã ya shahara da son gyãran abũbuwa dõmin islãhi, haka ne ga al'adar mutãne wanda ya tãshi yanã gyãra sai sun tuhumce shi da neman girma. ** Tanƙwasa ce sanya mutãne su yi abin da bã Su son yi. Kyautatãwar islãhi bã ta sãmuwa sai da tanƙwasãwa dõmin gãlibi mutãne sun fi son ɓarna a kan kyautatãwa tãre da saninsu ga cewar kyautatãwar ita ce daidai.
Kuma wani mutum ya zo daga mafi nĩsan birnin yanã taliya da gaggãwa, ya ce: "Ya Mũsã! Lalle mashãwarta sunã shãwara game da kai dõmin su kashe ka sabõda haka ka fita. Lalle nĩ, mai nasĩha ne a gare ka."
Sai ya fita daga gare ta,* yanã mai jin tsõro yanã sauna. Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Kã tsẽrar da ni daga mutãne azzãlumai."
____________________
 * Ya fita daga alƙaryar.
Kuma a lõkacin da ya fuskanci wajen Madyana, ya ce: "Inã fatan Ubangijĩna Ya shiryar da ni a kan madaidaiciyar hanya."
Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho* ne mai daraja."
____________________
 * Sabõda girma bã ya zuwa ya shãyar da tumakinsa, sai ya sanya mu, mu 'ya'yansa, kõ da muke mãtã. Wannan ya nũna mace tanã yin aikin maza sabõda larũra. Kuma sabõda darajar ubansu ba su shiga a cikin makiyãya ba dõmin tsaron mutuncinsu don haka ake son asali mai kyau. NĩSantarsu daga maza nau'in ƙauracewa ne na sharĩ'a.
Sai ya shãyar musu, sa'an nan kuma ya jũya zuwa ga inuwa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne."
Sai ɗayansu ta je masa, tanã tafiya a kan jin kunya, ta ce, "Ubãna yanã kiran ka, dõmin ya sãka maka ijãrar abin da ka shãyar sabõda mu." To, a lõkacin da ya je masa, ya gaya masa lãbãrinsa, ya ce: "Kada ka ji tsõro, kã tsĩra daga mutãne azzãlumai."
¦ayarsu ta ce, "Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi* amintacce."
____________________
 * Watau tanã iShãra ga ubantada cewa Mũsa ya tãra siffõfin nan biyu na ƙarfi da amãna dõmin abin da ta jarraba daga gare shi kafin ya iso ga ubanta.
Ya ce: "Lalle ne inã nufin in aurar da kai ɗayan 'yã'yãna biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijãra shẽkara takwas to, idan ka cika gõma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsanantã maka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga sãlihai."
Ya ce: "Wannan yanã a tsakanina da tsakãninka kõwane ɗayan adadin biyun na ƙãre, to, bãbu wani zãlunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa."
To, a lokacin da Mũsã ya ƙãre adadin kuma yanã tafiya da iyãlinsa, sai ya tsinkãyi wata Wutã daga gẽfen dũtse (¦ũr). Ya cewa iyãlinsa, "Ku dãkata, lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wutã, tsammãnĩna ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani lãbãrĩ, kõ kuwa da guntun makãmashi daga Wutar don kõ ku ji ɗimi."
To, a lõkacin da ya jẽ wurinta (Wutar) aka kirã shi, daga gẽfen rãfin na dãma, a cikin wurin nan mai albarka, daga itãciyar (cẽwa) "Ya Mũsã! Lalle Nĩ ne Allah Ubangijin halittu."
"Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta, tanã girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya jũya yanã mai bãyar da bãya, bai kõma ba. "Ya Mũsã! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsõro lalle ne kanã daga waɗanda ke amintattu."
"Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, ba da wata cũta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kãfaɗunka, dõmin tsõro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abũbuwa dalĩlai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da 'yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutãne ne fãsiƙai."
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle nã kashe wani rai daga gare su, dõmin haka inã tsõron kada su kashe ni."
"Kuma ɗan'uwana Hãrũna shĩ ne mafi fasãha daga gareni, ga harshe, sabõda haka Ka aika shi tãre da ni, yanã mai taimako, yanã gaskata ni, lalle ne inã tsõron su ƙaryata ni."
Ya ce: "Zã Mu ƙarfafa damtsenka game da ɗan'uwanka kuma Mu sanya muku wani dalĩli, sabõda haka bã zã su sãdu zuwa gareku ba, tãre da ãyõyinMu, kũ da waɗanda suka bĩ ku ne marinjãya."
To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko."
Kuma Mũsã ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara."
Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka* (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata."
____________________
 * Fir'auna ya fãra yin gasasshen tũbali da ake cewa ajurru, aka gina masa dõgon bene, ya hau samansa, ya harba kibiya ta tafi ama, ta kõmo da jini. Saĩ ya ce: "yã kashe Ubangijin Mũsa." Bayan haka sai benen ya karye guntu uku' guntu ɗaya ya fãɗa wa sõjansa, da yawa daga cikinsu suka mutu, guntu ɗaya kuma ya fãɗa a cikin ruwa, sauran guntu ɗaya ya fãɗa wa magina, suka mutu. Kuma cewar Fir'auna, "Lalle ne nĩ, inã zuton Mũsã daga maƙaryata," ya nũna girman kansa kawai ne ya hana shi ĩmãni, ba rashin gãnewa ba, sai dai kuma sun ga kamar bãbu Tãshin Ƙiyãma.
Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba.
Sai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance.
Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta, kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba.
Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu.
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa.
Kuma ba ka kasance ba ga gẽfen rãfi na yamma a lõkacin da Muka hukunta al'amaru zuwa ga Mũsã, kuma ba ka kasance daga halartattu ba.
Kuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa (da kai game* da waɗancan lãbarai).
____________________
  * Sanin waɗannan abũbuwa duka ga Ummiyyi a wuri mai nĩsa daga wurin da abin ya auku a ciki, da kuma nĩsa daga waɗanda abin ya fi shãfuwa, ya nũna gaskiyar abin da kake da'awa. Kuma yanã natsar da zũciyarka da zũciyar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira tãre da ku, cewa sunã cikin tsaron Allah.
Kuma ba ka kasance ga gẽfen dũtse ba a lõkacin da Muka yi kira, kuma amma dõmin rahama daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabãninka bai je musu ba, tsammãninsu sunã tunãwa.
Kuma bã dõmin wata masĩfa ta sãme su ba sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, su ce: "Yã Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bĩn ãyõyinKa, kuma mu kasance daga mũminai?"
Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga wurinMu, suka ce: "Don me ba a bã shi kamar abin da aka bai wa Mũsã ba?" Shin kuma ba su kãfirta ba da abin da aka bai wa Mũsã a gabãnin (wannan)? suka ce: "Sihirõri biyu ne suka taimaki jũna," kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mãsu kãfirta ne ga dukansu?"
Ka ce: "To ku zo da wani littãfi daga, wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bĩ shi, idan kunkasance mãsu gaskiya."
To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sãdar* da magana sabõda su, tsammãninsu, suna tunãni.
____________________
  * Attaura da Alƙur'ãni. Ayyukan Annabawa sãshenSu sun sãdu da sãshe.
Waɗanda Muka bã su littãfi daga gabãninsa (Alƙur'ãni), su mãsu ĩmãni ne da shi.*
____________________
  * Mun sãdar da ilmin Taurãta da ilmin Alƙur'ãni, kowãne ya gaskata wani, ko kuwa Mun sãdar da maganar Alƙur'ani, wata ta bi wata, babu bambanci ga fasãha da abũbuwan ban mãmaki a cikinsu.
Kuma idan anã karanta shi a kansu, sai su ce: "Mun yi ĩmãni da shi, lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinmu. Lalle mũ, mun kasance a gabãninsa masu sallamãwa."
Waɗancan anã ba su lãdarsu sau biyu, sabõda haƙurin da suka yi, kuma da kyautatãwa suna tunkuɗewar mũnanãwa kuma daga abin da Muka azũrtã susunã ciyarwa.
Kuma idan sun ji yãsassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, "Ayyukanmu sunã a gare mu, kuma ayyukanku sunã a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu bã mu nẽman jãhilai (da husũma)."*
____________________
  * Waɗanda aka bai wa littafi a gabãnĩn Alƙur'ãni, sũ ne Yahũdu da Nasãra,waɗansu daga cikin Malamansu sun musulunta, kamar Abdullahi bn salãmi daga Yahũdu, da Nasãran Najrãna daga Nasãra, sun musulunta. Idan ba'ali ya musulunta sai a ce dukansu ke nan sun musulunta, sai wanda ya yi girman kai ya ƙigaskiya. Bã zã a kula da shi ba.
Lalle ne kai bã ka shiryar* da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa.
____________________
 * Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, ya kasance yanã son mutãnensa Ƙuraishãwa su shiryu har dai Amminsa Abu Talib, sai Allah Ya gaya masa cewa shiriya ga hannunsa take, shi kaɗai, kuma sai wanda Ya so, shi ne zai shiryu, amma kuma akwai daga cikin dalĩlai bayyanannu maganar hijira kamar yadda ãyar da ke tafe ta bayyana.
Kuma suka ce: "Idan mun bi shiriya tãre da kai anã fizge mu(5) daga ƙasamiu." Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, anã jãwõwa zuwa gare shi, 'ya'yan itãcen kõwane iri, bisa ga azurtãwa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
____________________
 (5) Wanda ya makkana musu Hurumi ya zama amintacce, yanã iya tsare bãwanSa kuma Yabã shi arziki a kõ'ina yake a cikin ƙasa, sabõda haka tsõron fita daga Hurumi da tsõron wuyar abinci a wurin baƙunci, bã zai hana mũmini ya yi hijira da addininsa ba zuwa wurin yardar Allah.
Kuma da yawa Muka halakar da wata alƙarya wadda ta yi butulci ga rãyuwarta. To, waɗancan gidãjensu ne, ba a zaune su ba, a bãyansu, fãce kaɗan. Kuma mun kasance Mũ ne Magãda.
Kuma Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryu ba, sai Ya aika a cikin hedkwatarsu da wani Manzo yanã karanta ãyõyinMu a kansu. Kuma ba Mu kasance Mãsu halaka alƙaryu ba, fãce mutanensu sun kasance mãsu zãlunci.
Kuma abin da aka bã su daga kõme, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne da ƙawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shĩ ne mafi alhẽri, knma mafi wanzuwa. Shin bã ku hankalta?
Shin fa, wanda Muka yi wa wa'adi, wa'adi mai kyau, sa'an nan shĩ mai haɗuwa da shi ne, yanã zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan dãɗi, dãɗin rãyuwar dũniya, sa'an nan shi a Rãnar ¡iyãma yanã daga mãsu shiga wuta?
Kuma rãnar da (Allah) Yake kiran su sa'an nan Ya ce: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?"
Waɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan sũ ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mũ suke bautã wa ba."
Kuma a ce ku kirãwo abõkan tãrayyar ɗinku, sai su kira su, sai ba su amsa ba, kuma su ga azãbar. Dã dai lalle su sun kasance snnã shiryuwa*!
____________________
   * An shãfe jawãbi. ƘaddarawarSa ita ce: "Dã Sun kaSance sunã shiryuwa a dũniya, dã ba su gan ta ba a Lãhira.".
Kuma rãnar da Yake kiran su, sa'an nan Ya ce: "Mẽne nekuka karɓa wa Mananni?"
Sai lãbãru su ɓace musu a rãnar nan sa'an nan bã zã su tambayi jũnaosu ba.
To, amma wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni' ya aikata aiki na ƙwarai, to, akwai fãtan su kasance daga mãsu cin nasara.
Kuma Ubangijinka Yanã halitta abin da Yake so kuma Yake zãɓi. Zãɓi bai kasance a gare su ba. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.
Kuma Ubangijinka Yanã sanin abin da zukãtansu ke ɓõyẽwa, da abin da suke bayyanãwa.
Kuma Shĩ ne Allah, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kuma Shi ne abin gõdiya a cikin ta farko (dũniya), da ta ƙarshe (Lãhira). Kuma Shi ne da hukunci, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, bã ku ji?"
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kunã natsuwa a cikinsa? Shin fa, bã ku gani?"
"Kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini dõmin ku natsu a cikinsa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde."
Kuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: "Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa"*
____________________
  * Bãyan Allah Ya tunãtar da Musulmi rahamarSa da kaɗaita ga bãyar da ni'ima kõ hana ta da siffõfi mãsu kwaɗaitar da mũmini ga ɗã'a ga Allah da ManzonSa, daga cikin ɗã'ã akwai yin hijira wanda yake shĩ ne kan lãbãrin sũrar, sai kuma Ya tsõratar da mai bin wanin Allah ga rashin yin hijira. Duka abin da ya hana mũminai hijira idan shi abin nan ba uzuri ne na shari'a ba, to, ya zama gunki, abin bautãwa, wanin Allah. Umurnin da ya sãɓa wa umurnin Allah duka, umurnin abõkin tãrayya ne ga Allah ga wanda ya bĩ shi.
Kuma Muka zãre mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan Muka ce: "Ku kãwo dalilinku." Sai suka san cẽwa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya ɓace daga barinsu.
Lalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita* daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a** ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa."
____________________
   * Asalin baghy zãlunci, amma ga izɗilãhi, shi ne fita daga ɗã'ar shugaban Musulmi. ** Yawan su saba'in, an ce arba'in, kuma an ce gõma.
"Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa,* lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna."
____________________
  * Ɓarna a cikin ƙasa, shi ne fita daga tsarin jama'a, da rabasu ƙungiya-ƙungiya, ko barin hijira a bãyan an yi umurni da yin ta.
Ya ce: "An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai." Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba?*
____________________
   * Yanã ganin dũkiyar da ya samu, ya sãme ta ne sabõda ya san ilmin fatauci da sana'a kuma yanã da ƙarfin neman dũkiyar, sabõda raddin irin tunãninsa Allah Ya ce Ya halaka wanda ya fi shi tsananin ƙarfi da ƙõƙarin tãra dũkiya, kuma idan Ya tãshi halaka mai laifi bã Ya tsayãwa tambayarsa dalĩlin da ya sa ya yi laifin kãfin Ya halakar da shi. Waɗannan abũbuwa uku sun isa ga mai dũkiya ya yi tunãni, dõmin kada annashuwa ta shige shi ya ƙi gõde waAllah.
Sai (¡ãrũna) ya fita a kan mutãnensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rãyuwar dũniya suka ce: "Inã dai munã da kwatancin abin da aka bai wa ¡ãrũna! Lalle shĩ haƙĩƙa ma'abũcin rabo babba ne."
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai,* kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai ha ƙuri."
____________________
 * ĩmãni da aikin ƙwarai wanda Allah Ya yi umurni da a yi shi, kuma yinsa kamar yadda ManzonSa ya nũna. Akwai daga cikin aikin ƙwarai yin hijira da barin kula da dũkiya. Bã a sãmun sakamakon Allah sai da haƙuri.
Sai Muka shãfe ƙasa* da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba.
____________________
* An ce a bãyan Ƙãrũna ya yanke kansa da nasa mutãne daga Mũsã, sai ya shirya da wata kãruwa dõmin ta yi wa Mũsã ƙazafin cewa ya yi zina da ita, a kan ya aure ta. Sai Mũsãya tãshi yanã wa'azi a cikin Banĩ Isrã'ĩla ya ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla wanda ya yi sãta zã mu yanke hannunsa, wanda yayi ƙazafi mu yi masa bũlãla tamãnin, wanda ya yi zina, bã ya da mãtã, mu yi masa bũlãla ɗãri, wanda ya yi zina yanã da mãtã, mu jefe Shi sai yã mutu." Sai Ƙãruna ya ce: "Kõ dã kai ne?" Ya ce: "Kõ da ni ne." Sai Kãrũna ya ce: "An ce kã yi fãjirci tãre da wance, kãruwa." Sai Mũsã ya ce: "A kirã ta" Da ta zo, ya gama ta da Allah, ta faɗi gaskiya, sai ta ce Ƙãrũna ne ya yi tsãda da ita, ta faɗi hakanan. Sai Mũsã ya yi addu'a a kansa, ƙasa ta haɗiye shi, shi da gidansa duka.
Kuma waɗanda suka yi bũrin matsayinsa a jiya suka wãyi gari sunã cẽwa, "Wai! Allah Yanã shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bãyinsa, kuma Yanã ƙuntatãwa. Bã dõmin Allah Ya yi mana falala ba dã Yã shãfe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kãfirai bã su cin nasara."
Wancan gidan Lãhira Munã sanya shi ga waɗanda suke bã su nufin ɗaukaka a cikin rãyuwar dũniya kuma bã su son ɓarna. Kuma ãkiba ga mãsu taƙawa take.
Wanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alhẽri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mũgun abu, to, bã zã a sãkawa waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka ba, fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma. ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananna."
Kuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako* ga kãfirai.
____________________
  * Taimakon, shi ne ka yi bũrin musuluntarsu har ka wahala dõmin a sauƙaƙe ma hukuncin hijira wadda Allah Ya yi umurni da a yi ta a bãyan musulunta sai ka iyar da Manzanci, shiryarwa kuwa ga hannun Allah take. Wannan ãyã tanã nunãwa bayyana ƙaryar mãsu da'awar cewa wani mutum yanã bai wa wani ĩmãni ko ya karɓe shi daga gare shi. Kõwa a cikin tsõro yake, sai wanda Allah Ya sanya shi cikin aminci. Allah Ya sanya mu cikin amincinSa dõmin rahamarsa. 
Kuma kada lalle su karkatar da kai daga barin ãyõyin Allah, a bãyãn har an saukar da su uwa gare ka. Ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma kada lalle ka kasance daga mãsu shirka.
Kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kõwane abu mai halaka ne fãce fuskarSa. Shi ne da hukunci kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.*
____________________
 * Wannan ãyã ta ƙarshen sũrar, ta tãra ilmin da sũrar ta karantar a cikin abũbuwa biyar da ta zãna
Icon