ﰡ
Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi* daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.
____________________
* Saukar da malãiku da Rũhi watau Alƙur'ãni a zãmanin Annabci kõ kuma fahimta da ƙarfin zũciya waɗanda Allah ke sanyãwa ga wanda Ya nufa da jaddada addĩni a kan kõwane ƙarni. Aiko mãsu gargaɗi shĩ ne mafi girman ni'imar Allah a kan mutãne.
Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya.
Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci.
Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã.
Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai.
Kuma da dawãki* da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba.
____________________
* Haɗa dawãki da alfadarai zuwa ga jãkuna kuma aka ce dõmin "hawansu da yin ƙawã" yana nũna cewa ba a cin dawãki da alfadarai dõmin an san cewa an hana cin jãkuna a lõkacin yãƙin Khaibara, kuma ãyõyin da ke gaba da wannan ãya sun nũna anã cin dabbõbin ni'ima kuma anã hawansu, kuma cin nãma yã fi hawa zama ni'ima, sabõda haka, shĩ ne ya kamãta a ambata inda ya halatta. Wannan ne mazhabar Mãliki da Ahu Hanĩfa, kuma shĩ ne maganar Abdullah bn Abbãs Allah Ya yarda da su. Wasu sun ce ana cin dawãki da alfadarai dõmin cewa, "Anã hawansu dõmin ƙawa," bã ya hana a yi wani abu da su, wato cin nãmansu, dõmin a cikin Bukhãri daMuslim an ruwaito halaccin cin dawãki. Wannan shĩ ne maganar Al-Hasan da Shuraih da 'Aɗa' a da Sa'ĩd bn Jubair. Kuma Shi ne mazhabar shãfi'i da Is'hãƙ. Sun yi hujja da halaccin nãman dawãki da abin da Asmã'u bint Abĩ Bakar Assiddiƙ ta ce, "Mun sõke wata gõɗiya' muka ci a zamanin Manzon Allah,a Madina." Kuma a cikin Bukhãri da Muslim daga jãbir, Allah Ya yarda da shi, "Mun ci dawãki da jãkunan jeji a Khaibara, kuma Annabi tsira da aminci sun tabbata a gare shi, ya hana jãkunan gida" Acikin Abĩ Dãwud, "Mun yanke dawãki da alfadarai da jakuna alhãli yunwa ta kãmã mu, amma sai Annabi ya hana mu cin jãkuna da alfadarai, bai hana mu cin dawãki ba" Nĩ, a ganina, ra'ayin cin dawãki ya fi ƙarfi dõmin sũrar ta sauka a Makka, amma hadisin yankan gõɗiyar, a Madĩna aka yi shi. Saboda haka surar ba ta shãfe shi ba. Dũbi Radd Al-Azhãn.
Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacẽwa. Kuma da Yã so, dã Ya shiryar da ku gabã ɗaya.
Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dõminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itãce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo.
Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta.
Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai sãɓãnin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke tunãwa.
Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa.
Kuma Ya jẽfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dõmin kada ta karkata da ku, da kõguna da hanyõyi, ɗammãninku kunã shiryuwa.
Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci).
Shin, wanda Yake yin halitta yanã yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bã ku tunãwa?
Kuma idan kun ƙidãya ni'imar Allah, bã ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke asirtãwa da abin da kuke bayyanãwa.
Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kõme ba, kuma sũ ne ake halittawa.
Matattũ ne, bã su da rai, kuma ba su san a wane lõkaci ake tãyar da su ba.
Abin bautawarku, abin bautãwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, zukãtansu mãsu musu ne, kuma su makangara ne.
Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yanã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. Lalle ne Shi, bã Ya Son mãsu girman kai.
Idan aka ce musu: "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Sai su ce: "Tãtsũniyõyin mutãnen farko."
Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar ¡iyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana.
Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa,* sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba.
____________________
* Kamar yadda Allah Ya halaka Bukht Nasar. Aka halaka shi da ginin gidansa. Allah Yanã halaka kãfirai da abin da suke tãnadã wa kansu dõmin nħman rãyuwarsu.
Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kãfirai."
Waɗanda malãiku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu zãluntar kansu. Sai suka jẽfa nẽman sulhu (suka ce) "Ba mu kasance muna aikata wani mummũnan aiki ba." Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Sai ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kunã madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin mãsu girman kai.
Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan mãsu taƙawa.
Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke sãkã wa mãsu taƙawa.
Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
Sai mũnãnan abũbuwan da suka aikata ya sãme su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.
Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã?
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.
Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah bã Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma bã su da waɗansu mataimaka.
Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bã ya tãyar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
Dõmin Ya bayyana musu abin da suke sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin waɗanda suka kãfirta su sani cẽwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryatã.
Abin sani kawai, MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, "Ka kasance; sai yanã kasancẽwa.
Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su, haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi girmã, dã sun kasance sunã sani.
Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.
Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, fãce waɗansu mazãje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutãnen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba.
Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãninsu su yi tunãni.
Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba?
Ko kuwa Ya kama su a cikin jujjuyawarsu? Sabõda haka ba su zama masu buwãya ba.
Ko kuwa Ya kama su a kan naƙasa? To, lalle ne Ubangijinka haƙĩƙa Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu ƙasƙantar da kai?
Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma bã su kangara.
Suna tsõron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umuruin su.
Kuma Allah Ya ce: "Kada ku riƙi abũbuwan bautãwa biyu. Abin sani kawai, wanda ake bautãwa guda ne, sa'an nan sai kuji tsõroNa, Ni kawai."
Kuma Yana da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, kuma Yana da addini wanda yake dawwamamme. Shin fa, wanin Allah kuke bĩ da taƙãwa?
Kuma abin da yake a gare ku na ni'ima, to, daga Allah ne. Sa'an nan kuma idan cũta ta shãfeku, to, zuwa gare Shi kuke hargõwa.
sa'an nan idan Ya kuranye cũtar daga gare ku, sai gã wani ɓangare daga gare ku game da Ubangijinsu sunã shirki.
Dõmin su kãfirta da abin da Muka bã su. To, ku ji dãɗi, sa'an nan da sannu zã ku sani.
Kuma sunã sanya rabõ *ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa.
____________________
* Sunã sanyãwar rabõ daga dabbõbi da hatsi ga gumãka kõ aljannu, alhãli ba su san amfãnin da gumãkan kõ aljannun suke iya jãwo musu ba kõ suke tunkuɗewa daga gare su. Akwai daga cikin ni'imõmin Allah, Ya shiryar da mutãne ga gãne cewa waɗannan gumãka da aljannu kõ wani mahalũƙi bã ya iya cũta kõ jãwo wani amfãni fãce da iznin Allah. Sabõda haka bãbu wanda ya cancanci a bauta masa fãce Allah, Mai tumɓuke cũta kuma Mai jãwo amfãni. Watau wannan bãyar da ni'imar 'yancin ɗan Adam kãmilan, su duka bãyi ne, bãbu daraja ga kõwa sai da taƙawa.Sanin haka wata ni'ima ce daga Allah.
Kuma sunã danganta 'ya'ya mãta ga Allah. Tsarkinsa yã tabbata! Kuma sũ ne da abin da suke sha'awa.
Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace* sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki.
____________________
* Fahintar cewa ɗã namiji da'ya mace duka ɗaya suke, da hana kashe su kõ turbuɗe su, wata ni'ima ce babba da 'yancin mãtã babba, a cikin rãyuwar ɗan Ãdam.
Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana.
Ga waɗanda ba su yi ĩmãni* da Lãhira ba akwai sifar cũta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.
____________________
* Ƙãrin bãyani ne ga abin da ya gabãta kuma na bãya da shi ya rãtayu da shi, shiryarwa zuwa ga halãye maɗaukaka ni'ima ce babba.
Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu,* dã bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta ba.
____________________
* Rashin halaka dũniya sabõda laifin mutãne da rashin kãmasu da dukan laifinsu, ni'ima ce babba.
Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlẽwa ne (a cikinta).
Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabãninka, sai Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre.
Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima; Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã.
Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye* da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.
____________________
* Yã ambaci abin mãye a cikin abũbuwan ni'ima a gabãnin aharamta giya. Kuma haramtã ta bã ya hanã ta zuma a cikin ni'imõmin Allah ga mutãne dõmin an haramtã ne sabõda tsaron hankalinmu a kan neman waɗansu ni'imõmin da suka fĩ ta a Aljanna a inda bã zã a hana ta ba sabõda ƙarewar taklĩfi a can. Sabõda haka ne ya ƙãre ãyar da cewa: "Akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.".
Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi* zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa."
____________________
* Wahayi na ilhama, watau Allah Ya cũsa wa ƙudan zama ilmin yin sã ƙar gidan zuma da gãne hanyõyin tafiya ta kõma gidanta, da cin kõwane irin furen itãce dõmin a fitar dani'imar abin sha mai dãdi ga mutãne, kuma wanda ya ƙunsa dukkan mãgani ga ciwarwatansu. Wannan ni'ima ce babba.
"Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi.
Kuma Allah Ya fifita sãshenku* a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu?
____________________
* Arziki daga Allah yake, yanã fĩfĩta waɗansu bãyinsa da arziki a kan waɗansu, sa'an nan wanda aka bai wa arziki daga ckinsu bã ya iya mayar da arzikin a tsakãninsa da wani bãwa nasa har su zama daidai a kan arzikin. to, idan haka ne, yaya kuke sanya waɗansu bãyin Allah daidai da Allah wajen bautarku gare su?.
Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta?
Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa (ga aikata kõme).
Sa'an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba.
Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme, da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba.
Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici?
Kuma ga Allah gaibin* sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne.
____________________
* Ɓõye lõkacin Ƙiyãma a bãyan bayãnin tabbatar aukuwarta yanã daga cikin ni'imõmin Allah, dõmin mai hankali ya yi tattãli sabõda ita.
Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde.
Shin ba su ga tsuntsãye* ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
____________________
* Tsuntsãye hõrarru a cikin sararin sama, ana nufi da su, a ganĩna, Allah ne Ya san haƙĩƙa, su ne jirãgen sama, sabõda ambaton hõrewa tãre da sũ a cikin sararin samãniya, dõmin abin da aka hõre, ana hõronsa ne dõmin a ci amfãninsa a lõkaci da wurin hõron. Tsuntsãyen al'ãda bã su da wani amfãni a gare mu a lõkacin da suke a cikin sãrãrin sama. Sabõda haka bãbu wani abu, sai jirgin sama. Bã zã a ce anã nufin shãho ba a lõkacin farauta, dõmin wannan amfãni yã yi kaɗan bisa ga abin da sũrar take ƙidãyãwa na ni'imõmin Allah a kan mutãne gabã ɗaya. Farauta keɓãɓɓiya ce ga mutãnen ƙauye kawai.
Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu* da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci.
____________________
* Sũfi, shi ne gãshin tumãki mai kama da audugã, wabar shi ne gãshin rãƙumi mai laushi, sha'ar, shi ne gãshin awaki da gezar dawãki. Bai ambaci audugã da kattãni ba, dõmin a wajen shũka suke.
Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna *sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa.
____________________
* Rĩgã dõmin zãfi da sanyi daga sũfi da wabar da gãshi da audugã da kattãni da rĩga dõmin makãmi shi ne sulke, dõmin makãmi daga baƙin ƙarfe yake kamar takõbi, mãshi da kibiya.
To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã.
Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne.
Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba.
Kuma idan waɗanda suka yi zãlunci suka ga azãba, sa'an nan bã za a saukake ta daga gare su ba, kuma bã su zama anã yi musu jinkiri ba.
Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne."
Kuma su shiga nẽman sulhu zuwa ga Allah a rãnar nan, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace daga gare su.
Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange daga hanyar, Allah, Mun ƙãra musu wata azãba bisa ga azãbar, sabõda abin da suka kasance sunã yi na fasãdi.
Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al'umma a kansu daga kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littãli a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi).
Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa.
Kuma ku cika da alkãwarin* Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa.
____________________
* Wanda yake rantsuwar alkawari da wani, sa'an nan ya warware rantsuwar dõmin neman ya ƙulla wata rantsuwa da wani mutum sabõda wani amfãninsa kõ jama'arsa a cikin wata kabĩla wadda ta fi ta mutãnen farko ƙarfi to, siffarsa kamar mace ce mahaukaciya, mai yin zare, a bayan ta tukka shi, ya yi ƙarfi, sa'an nan ta warware shi. Sabõda haka idan ta so mayar da shi wani zare, to, bã zai yi kyau ba kamar zaren farko da ta yi kuma mutãne sun gãne haukarta, bã zã su yi wata ma'ãmala da ita ba. Wanda ya yi rantsuwa da Allah a kan abu, to, yã sanya Allah lãmuni ke nan. Bã ya halatta ga wanda ya shugabantar da Allah ga wani abu, sa'an nan ya kõma bãya ya ƙi cika wannan alkawarin dõmin bai kiyãye girman Allah ba, wanda ya sanya a tsakaninsa da abõkin ma'ãmalarsa. Tsaron alkawari ni'ima ne.
Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bãyan tukka, ya zama warwararku, kunã riƙon rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, dõmin kasancẽwar wata al'umma tãfi rĩba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yanã jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yanã bayyana muku a Rãnar ¡iyãma, abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wajũna.
Kuma dã Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dã Ya sanya ku al'umma gudã, kuma Yanã ɓatar da wanda Ya so. kuma Yanã shiryar da wanda Ya so. Lalle ne anã tambayarku abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Kada ku riƙi rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma.*
____________________
* Wanda yake yin rantsuwa da Allah dõmin ya yaudari wani, to, yanã rũsa kansa ne da kansa, kuma Allah Yanã ħbe jãrumci da natsuwa daga zũciyarsa, sa'an nan kuma yanã da wata azãba mai girma a Lãhira idan Allah bai gãfarta masa ba, da tũba kõ da wani sababi. Sanin haka ni'ima ne.
Kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.
Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Sa'an nan idan ka karantã *Alƙur'ãni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe.
____________________
* An yi saɓãni ga zaman Isti'ãza gabãnin karãtu kõ a bãyansa. Mãlik ya zãɓi a yi 'Isti'ãza' bãyan karãtu, kõ a bãyan an ƙãre yin salla, dõmin kada shaiɗan ya rinjãyi mutum a bãyan ĩmãninsa da salla. Sabõda haka ya karhanta shi a cikin salla. Wasu kuma sunã isti'ãzã a gabãnin karãtu kõ a gabãnin salla.
Lalle ne shi, bã shi da wani ƙarfi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu.
Abin sani kawai ƙarfinsa yanã a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, mãsu shirki ne.
Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne." Ã'a, mafi yawansu bã swa sani.
Ka ce: "Rũhul ¡udusi* ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma (dõmin) shiriya da bushãra ga Musulmi."
____________________
* Rũhul Ƙudusi, watau rai mai tsarki, anã nufin Jibrilu, amincin Allah ya tabbata a gare shi.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin (cẽwa) lalle ne sũ, sunã cẽwa, "Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi." Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan (Alƙur'ãni) harshe ne Balãrabe bayyananne.
Lalle ne waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, Allahbã zai shiryar da su ba, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
Abin sani kawai waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata.
Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma.
Waɗancan ne kãfirai dõmin sun fĩfĩta son dũniya a kan Lãhira, kuma lalle ne Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.
Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukãtansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗancan sũ ne gafalallu.
Bãbu shakka lalle ne a Lãhira sũ ne mãsu hasãra.
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba.
Kuma Allah Ya buga misãli,* wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.
____________________
* Kamar Makka. Annabi Muhammadu ya je musu sun ƙaryata shi, sai Allah Yã musanya amincinsu da tsõro, kuma wadãtarsu da yunwa. Wannan shĩ ne sakamakon ridda a kõwane lõkaci.
Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci.
Sa'an nan ku ci daga* abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa.
____________________
* Bãyan bayãni a kan hukuncin ridda sabõda sanyãwar sãshen ni'imõmin Allah ga wasu gumãka kõ aljannu kõ waɗansu mutãne sãlihai, sa'an nan Ya yi umurni da cin abin da Allah Ya azurta mutum duka amma da sharuɗɗa uku, watau ya zama halas ga shari'a kuma mai dãɗin ci, wani haƙƙi na wani mutum bai rãtaya ba a kansa ga shari'a, kuma a bi shari'a wajen aikatar da shi kamar yadda Allah Ya ce wajen yanka da mai kama da shi, shi ne gõde wa Allah. Sabõda haka banda kamar giya da kãyan wani mutum sai fa a bisa yardarsa.
Abin sani kawai (Allah) Ya haramta* muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
____________________
* Bayãnin abũbuwan da aka haramta, idan bãbu larũra. Anã cin abin da shari'a ta hana a ci a kan larũra sai idan larũrar ta sãmi mutum ne a cikin hãlin sãɓon Allah, kamar mai fita daga ɗã'ar sarkin Musulunci ya yi tãsa ƙungiya dabam, kõ wanda ya fita dõmin wani zãlunci kamar sãta ga misãli, to, ba su cin haram dõmin su ci gaba da aikinsu.
Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba.
Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi.
Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni,* kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta.
____________________
* Gabãnin wancan sũra, kamar a cikin sũratul An'ãm ãyã ta l46. Sabõda haka bã a biyar da Yahũdu a wajen haramcin abin da Allah Ya haramta musu, su kaɗai sabõda zãluncinsu.
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki* da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
____________________
* Wanda ya yi wani abu da Allah Ya hana wajen ni'imõmi ko wajen wani abu dabam na sãɓon Allah, to, idan ya tũbã A gabãnin ya kai ga gargara, Allah zai gãfartã masa. Wannan ni'ima ce.
Lalle ne Ibrãhĩm* ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.
____________________
* Akwai daga ni'imõmin Allah,Ya sanya mutum maɗaukaki sabõda addininsa da ĩmãninsa ga Ubangijinsa, kuma Yã bã shi ĩkon binsa da taƙawa kamar yadda Ya yi wa Ibrahĩm. Kuma akwai daga ni'imõmin Allah Ya sanya mutum a cikin zuriyyar mutumin kirki kamar yadda Ya yi wa Annabi Muhammadu Ya sanya shi a cikin zuriyyar Ibrãhĩm.
Mai gõdiya* ga ni'imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici.
____________________
* An ambaci Ibrãhĩm sabõda ya gõde wa ni'imõnin Allah dõmin Musulmi su yi kõyi da shi wajen gõde wa Allah ga ni'imõmin da Ya yi ishãra zuwa gare su a cikin wannan Sũra da watanta. Gõde wa ni'ima wata ni'ima ce.
Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai.
Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cẽwa), "Ka* bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.'
____________________
* Yanã cikin ni'ima ga Ibrãhĩm da kammalarta a gare shi a umurci mafĩfĩcin tãlikai Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, da bin aƙĩdar Ibrãhĩm.
Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa.(5) Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã.
____________________
(5) Waɗanda suka sãɓa wa jũna a cikin sha'anin Ibrahĩm wanda yake ya kasance yanã girmama Juma'a dõmin ita ce rãnar cikon ni'imõmin Allah a kan bãyinsa. Yahudu suka sãɓã wa Ibrãhĩm suka girmama Asabar dõmin a rãnar nan ne bãbu wani aiki. Wannan ya dõge har a bãyan ɗauke Ĩsa. Nasãra suka jũya dõmin ƙin Yahũdu zuwa ga Lahadi, dõmin su yi daidai da Kaisara, Ƙustantin, mai girmama Lahadi, rãnar bautã wa rãnã. Kafirce wa ni'ima azaba ce.
Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima(6) da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
____________________
(6) Kira zuwa ga hanyar Ubangiji, Allah, yanã daga cikin abũbuwan kõyo daga Ibrãhĩm kuma kira zuwa ga Allah na daga cikin ni'imõmin Allah ga mai kiran da wanda ake kiran sa'an nan zaman kiran da hikima da wa'azi mai kyau, ni'ima ce ga mai yi da waɗanda ake kira zuwa ga shiriyar duka. Abin da ake cħwa Hikima shĩ ne a yi magana a kan hujja wadda abõkin husũma bã zai iya kauce mata ba.
Kuma idan kuka sãka(7) wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri.
____________________
(7) Kuma mai kiran mutãne zuwa ga Allah lalle ne sai ya haɗu da cũtarwa daga mutãnen da bã su son gaskiyã. To, Allah bã Ya son zãlunci ko dã a kan maƙiyansa, sabõda haka Ya yi umurni da yin ƙisãsi da misãlin uƙũba, kõ a yi haƙuri, amma yin haƙuri yã fi rãmãwa dõmin nħman ni'imar Allah ta ƙãra kammala.
Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci.
Lalle Allah Yanã tãre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ mãsu kyautatãwa ne.