ترجمة معاني سورة المؤمنون باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية

الترجمة الهوساوية

الناشر

مجمع الملك فهد

آية رقم 1
Lalle ne, Mũminai* sun sãmi babban rabõ.
____________________
 * Mũminai su ne waɗanda suke da siffõfin da aka jeranta a cikin ãyõyĩn da ke biye daga ta 2 zuwa ga ta 9.
آية رقم 3
Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne.
آية رقم 5
Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne.
آية رقم 7
Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi.
آية رقم 8
Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
آية رقم 11
Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi,* su a cikinta madawwama ne.
____________________
 * Asalin firdausi fadama mai ruwa da itãce da ni'ima. Aljannar firdausi ita ce mafi ɗaukakar Aljanna.
آية رقم 13
Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.
Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa.
آية رقم 16
Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar ¡iyãma, za a iãyar da ku,
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba.
Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci.
Da wata itãciya,* tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ.
____________________
 * Itãciyar Zaitũni. Ita ce itãciyar farko da ta tsira a kan ƙasa a bãyan Ɗũfãna tanã rãyuwa mai dõgon lõkaci; an ce tanã rãyuwa kamar shekara dubũ huɗu. Anã cin 'ya'yanta, anã man shãfãwa da su, kuma anã yin miya dasu. Asalin sibg, rini dõmin tanã rina lõmar tuwo. Dũtsen Sĩnã'a mai albarka, ɗũr, shĩ ne dũtSe mai itãce a kansa.
Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni* mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ
____________________
  * Sũfi da gashi dõmin tufãfi da kãyan ɗãki, kãsũsuwa da fãtu da kõfatai dõmin yin abũbuwan amfãni.
آية رقم 26
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka taimakeni Saboda mutãnena sun ƙaryatã ni."
Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne.
آية رقم 29
"Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.'"
آية رقم 30
Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙẽƙa' Mãsu jarrabãwa.
آية رقم 34
"Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne."
"Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne?"
"Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa,* kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
____________________
 * Munã mutuwa kuma munã rãyuwa da haihuwar ɗiya da 'yã'ya. A bãyan wannan bãbu wata rãyuwa ta wata Lãhira,.
آية رقم 39
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni."
آية رقم 40
Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma."
Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai!
آية رقم 45
Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyinMu da, dalĩli bayyananne.
آية رقم 46
Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya.
آية رقم 47
Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne."
آية رقم 48
Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku.
آية رقم 49
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu* zã su shiryu.
____________________
 * Banĩ Isrã'ĩla na yanzu idan sun tuna cewa Alƙur'ãni bã shĩ ne farkon littafin sama ba, an bai wa Mũsã wani littafi, su kuma sunã alfahari da shi.
Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã* Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari.
____________________
* Ãyar Ĩsã da uwarsa ita ce an haife shi bãbu uba. Kuma a lõkacin nan Yahũdu suka so sarkin zãmanin nan ya kashe shi, sai uwarsa ta gudu da shi zuwa Baitil Maƙaddas, kõ Dimashƙa, kõ Falasɗĩnu, inda suka zauna shekara gõma sha biyar har sarkin nan ya mutu.
Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi* kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
____________________
  * Allah Ya umurci ManzanninSa da cin halat sa'an nan su aikata aikin ƙwarai. Haka kuma Ya umurci Mũminai. Sabõda haka karɓar aiki na ƙwarai an tsayar da shi ne a kan cin halat.
آية رقم 52
Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa.*
____________________
 * Taƙawa, ita ce bautawa Allah da abin da Ya yi umurni a bauta Masa, a kan harshenAnnabinsa na zamaninsa. Yanzu bãbu taƙawa sai a cikin Musulunci kawai.
Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu,(5) kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.
____________________
 (5) Kõwa ya kãma hanyarsa, al'ummar Musulmi ta zama ƙungiyõyi dabam-dabam, kõwanensu yanã farin ciki da abin da ke gare shi, yanã ganin shi ne mafifici
Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu,
آية رقم 61
Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri).
Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya.
آية رقم 67
Kunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha.
Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton* (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa.
____________________
  * Zikiri a nan, shi ne Alƙur'ãni wanda ya zo wa Lãrabãwa kõ Ƙuraishawa da abũbuwa na ɗaukakarsu, da ambatonsũnansu, da shiryar da su, da gabãtar da su a kan sauran kabĩlu. Amma duk da haka sunã bijirewa daga gare Shi.
Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa.
آية رقم 73
Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya.
آية رقم 76
Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba* sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u.
____________________
  * Azãbar dũniya kamar yunwa da ciwo da talauci da rashin kwanciyar hankali.
Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi.*
____________________
  * Mugi, shi ne kãsa yin magana sabõda ɗebe tsammãni daga sãmun kõwane alheri. Asalin kalmar daga Fulãtanci take.
Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba?
آية رقم 82
Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lale ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne?
آية رقم 87
Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba?"
آية رقم 90
Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
آية رقم 92
Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.
آية رقم 93
Ka ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi."
آية رقم 95
Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi.
آية رقم 98
"Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni,* "
____________________
  * Inã neman tsari da Kai, yã Ubangijina! Kada Shaiɗãnu su halarto ni a cikin al'amurana duka, dõmin ba su halarta, fãce da sharri.
Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba.
آية رقم 102
To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama.
آية رقم 104
Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne.
آية رقم 105
"Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa?"
آية رقم 106
Suka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwamiu ce ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu."
آية رقم 107
"Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci."
آية رقم 108
Ya ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana."
Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi."
آية رقم 110
Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõNa kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya.
آية رقم 111
Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
آية رقم 115
"Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba?"
آية رقم 118
Kuma ka ce: "Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama."
تقدم القراءة