ترجمة معاني سورة البلد
باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية
.
من تأليف:
أبو بكر محمود جومي
.
ﰡ
Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari* ba.
____________________
* Allah Ya ce ba sai Ya yi rantsuwa da Makka ba, sa'an nan zã a san darajarta a lõkacinda Annabi yake a cikinta, kuma shi yana da haƙƙin zama a cikinta mahaifansa da zurriyarsa duka, ko da yake zai yi hijira sabõda fitinar kãfirai mãsu halaka dũkiyarsu kan adãwa da shi. Dã sun yi amfãni da dukiyar ga ayyukan alheri, dã yã fi musu.
Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.
Da mahaifi da abin da ya haifa.
Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.
Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?
Yana cẽwa "Na* halakarda dũkiya mai yawa,"
____________________
* Nã halaka dukiya mai yawa dõmin faɗã da addĩni.
Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?
Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?
Da harshe, da leɓɓa biyu.
Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi* biyu ba?
____________________
* Hanyar alheri da ta sharri.
To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?
Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?
Ita ce fansar wuyan bãwa.
Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.
Ga marãya ma'abũcin zumunta.
Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.
Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.
Waɗannan ne ma'abũta albarka*
____________________
* Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da dãma, a Lãhira.
Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci(5)
____________________
(5) Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da hagu, a Lãhira.
A kansu akwai wata wuta abar kullewa.