ترجمة سورة الشمس

الترجمة الهوساوية
ترجمة معاني سورة الشمس باللغة الهوساوية من كتاب الترجمة الهوساوية .
من تأليف: أبو بكر محمود جومي .

Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.
Kuma da wata idan ya bi ta.
Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.
Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.
Da sama da abin da ya gina ta.
Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.
Da rai da abin da ya daidaita shi.
Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa.
Lalle ne wanda ya tsarkake* shi (rai) ya sãmi babban rabo.
____________________
 * Karɓar imãni da aiki da abinda ya ƙunsa tsarkake rai ne.
Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe* shi (da laifi) ya tãɓe.
____________________
* Kãfirci turbuɗe rai ne da zunubi.
Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.
A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).
Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).
Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).
Icon